
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An kama malaman asibiti guda biyu bisa hannu a mutuwar wasu ƙananan yara mata biyu ‘yan gida ɗaya bayan zargin ba su maganin da bai dace da rashin lafiyarsu ba a Babban Asibitin Gwamnati da ke Zuru a Jihar Kebbi.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda abin ya shafa masu shekaru shida da uku, sun rasu ne a ranar 18ga watan Maris, bisa zargin sakaci daga ɓangaren ba su magani a asibitin.
A yanzu haka waɗanda ake zargi da laifin suna hannun hukumar ‘yan sanda, inda ake gudanar da bincike akansu domin gano haƙiƙanin abin da ya sabbaba mutuwar yaran.
Akan wannan al’amari ne Gwamnatin Jihar Kebbi ta samar da kwamitin mutane tara domin gudanar da bincike ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Labarai da Al’adu na jihar, Alhaji Yakubu Ahmed. Tuni dai kwamitin ya fada zama a Zuru.
Haka kuma, gwamnatin jihar ta bayar da tallafin Naira miliyan 10ga iyalan mamatan domin rage musu raɗaɗin rashin ‘ya’yan nasu.
Mai Martaba Sarkin Zuru, Alhaji Mohammed Sanusi Mikailu Sami ya kirayi iyalan da su ɗauki al’amarin a matsayin ƙaddara da Allah, yana mai yaba wa Gwamna Nasir Idris na jihar bisa gaggauta ɗaukar mataki akan al’amarin.
