ICPC ta saki El-Rufai na wucingadi don halartar jana’izar mahaifiyarsa

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya samu sakin wucin gadi daga hannun hukumar ICPC. An ce an bayar da wannan damar ne domin ya samu halartar jana’izar mahaifiyarsa, Hajiya Umma, wadda ta rasu a birnin Cairo na ƙasar Masar.

Majiyoyi sun nuna cewa an amince da sakin nasa ne bisa dalilan jin ƙai sakamakon rasuwar mahaifiyarsa, duk da cewa ICPC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da lamarin. Ɗansa, Bashir El-Rufai, shi ne ya bayyana hakan ta shafinsa na sada zumunta, inda ya nuna godiya ga waɗanda suka nuna goyon baya ga iyalinsu a wannan lokaci.

Sai dai El-Rufai na fuskantar shari’o’i da dama da suka shafi zarge-zargen almundahana da kuma karya dokokin tsaro, kuma yana tsare tun watan Fabrairun 2026. An riga an gurfanar da shi a gaban kotu kan wasu tuhume-tuhume, inda ya musanta aikata laifukan, yayin da ake sa ran ci gaba da shari’ar bayan wannan sakin na wucin gadi.

By ukarofi