2027: Kwankwaso da Aregbesola sun gana a Abuja kan yiwuwar shiga ADC

Spread the love

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da sakataren jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, a birnin Abuja, lamarin da ke ƙara janyo hasashe a fagen siyasar Najeriya gabanin zaɓen shekarar 2027.

Rahotanni na cewa ana rade-radin cewa jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa na duba yiwuwar komawa jam’iyyar ADC a wani ɓangare na sabuwar haɗakar siyasa da ake shirin yi kafin zaɓen gaba.

Haka kuma, wasu rahotanni sun ce ana maganar yiwuwar haɗakar siyasa tsakanin Kwankwaso da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, domin tsayawa takarar shugaban ƙasa tare a zaɓen 2027.

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga ɓangarorin da abin ya shafa, amma masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa wannan ganawa na iya zama wata alama ta sabuwar haɗakar siyasa a Najeriya.

By Babaji