
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gidauniyar Kannywood Ta yi alhinin rasuwar Aliyu Sambo, wanda ɗaya ne daga cikin dattawan masana’antar Kannywood kuma ɗaya daga cikin manyan jami’anta masu barin gado.
Ta ce, marigayin yi taka rawa a wasannin kwaikwayo na dabe da kuma na talbijin sannan kuma ya taka rawa a wasannin kwaikwayo mai dogon zangon na Kwana Casa’in da kuma Zaɓi biyu a kwanan nan.
A wata sanarwa da Daraktan yaɗa labaran gidauniyar, Yakubu Liman ya fitar, gidauniyar ta bayyana cewa marigayin ya kasance mai jajircewa da aiki tuƙuru da kuma nuna halayya na gari a mu’amalarsa da ’yan uwa da kuma sauran abokan aiki musamman a lokacin da yake riƙe da muƙami a gidauniyar.
A cewarsa, “a tsawon rayuwarsa na aiki, ya taimakawa wannan gidauniya, ya kuma bayar da muhimmiyar gudunawa ga masana’antar Kannywood baki ɗaya.”
Don haka ta miƙa ta’aziyyarta tare da yi masa addu’ar fatan samun gafarar Allah SWT.
Haka kuma ta yi wa iyakansa jaje da fatan Allah ya ba su haƙurin juriyan rashin.
