Gwamna Raɗɗa ya kai ziyarar ta’aziyya ga El-Rufa’i kan rasuwar mahaifiyarsa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya kai ziyarar ta’aziyyar ga tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i a gidansa dake Aso Drive a babban birnin tarayya Abuja.

Allah ya yima mahaifiyar Malam Nasir El-Rufa’i rasuwa da yammacin ranar Juma’a 27/3/2026, a wani asibiti da ke ƙasar Masar (Egypt) bayan tayi fama da rashin lafiya.

Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya yi addu’a, Allah ya jiƙan ta da rahama yasa ta huta, ya kuma sanya aljanna fiddausi ce makomarta.

By ukarofi