
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya koma gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna domin sauraron buƙatar bayar da belinsa.
Hukumar ICPC ce ta gurfanar da shi a gaban Mai shari’a Rilwan M. Aikawa akan tuhume-tuhume guda 10 da suka haɗa da zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma zamba a lokacin da yake gwamnan jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa, an sako shi daga tsare ne a baya-bayan nan bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ta rasu a birnin Cairo na ƙasar Masar a ƙarshen makon da ya gabata.
A baya dai Kotu ta sanya ranar 31 ga Maris, 2026 domin sauraron duk wasu buƙatu da ke gabanta ciki har da neman beli da lauyoyin tsohon gwamnan suka gabatar mata.
Da fari, hukumar EFCC ne ta tsare shi bisa zargin sa da hannu a karkatar da akalar Naira biliyan 423, inda a ranar 18 ga Fabrairu ne aka sake shi. Saidai, bayan haka ne nan da nan hukumar ICPC ta sake kama shi.
