Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ɗan Majalissa mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Aliyu Abubakar Albaba shi ne ya gabatar da ƙudurin, inda yace matsalar ƙauranci na addabar al’ummar garin Katsina, inda ya bada misalai na irin mummunan aika aika da ƙauraye su keyi, wanda yake jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.
Majalisar ta bawa kwamitin tsaro na majalissar sati ɗaya, da yaje yayi bincike, ya kawo rahoto akan hanyoyin da ya kamata abi na doka domin a magance matsalar. Kwamitin zai haɗa kai tare da jami’an tsaro na jihar Katsina, domin samo hanyar da za’a magance matsalar.
Ka zalika kwamitin ƙananan hukumomi da masarautu na majalissar, ya gabatar da rahoto tare da cikakken bayani akan kasafin kuɗin shekarar 2026, na ƙananan hukumomi 34 dake jihar Katsina, a bisa tsarin dokar kasafin kuɗin ƙasa da ƙasa wato (IPSAS)
Shugaban kwamitin, Hon. Ibrahim Danjuma Machika shine ya gabatar da rahoton, a yayin zaman majalissar inda kwamitin ya jinjinawa Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa bisa yadda ya bawa ƙananan hukumomi gashin kansu suka samu damar gudanar da ayyukan raya ƙasa a ƙananan hukumomin su.
Matsalar ƙauraye a garin Katsina ana danganta shi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
Makon da ya wuce sai da aka rasa rayukan sakamakon hare haren ƙaurayen a unguwanni Unwala dake cikin garin Katsina.
