Gwamnatin Katsina za ta ɗauki ƙarin malaman makaranta 2,158

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya amince da ɗaukar sabbin malaman makaranta 2,158 domin cike guraben da ake da su a makarantun gwamnati a faɗin jihar.

Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta bayyana cewa, daga cikin adadin da za a ɗauka, malamai 1,500 za a tura su makarantun firamare, yayin da 658 za su koyar a makarantun sakandare.

Gwamnatin ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin inganta harkar ilimi a jihar, musamman wajen rage giɓin adadin malamai da ɗalibai da kuma ƙarfafa ingancin koyarwa a matakin firamare da sakandare.

Kwamitin da gwamnati ta kafa domin gudanar da aikin ɗaukar malaman ya buɗe ƙofar karɓar aikace-aikace daga ‘yan asalin jihar da suka cika ƙa’idojin da ake buƙata, domin cike guraben da aka tantance a wasu makarantu bisa la’akari da darussan da ake buƙata.

By ukarofi