
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon mataimakin gwamna kuma ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a zaɓen 2023, Nasiru Gawuna ya fice daga jam’iyyar APC a hukumance.
Ana sa ran wannan matakin zai kawo sauyin alƙiblar siyasar Gawuna musamman bisa la’akari da sauye-sauyen jam’iyya acikin ‘yan siyasa yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.
Gawuna ya fice daga jam’iyyar APC ne bayan ya ajiye muƙaminsa na shugabancin bankin lamuni na ƙasa (FMBN).
Duk da cewa Gawuna bau bayyana matakin siyasarsa ba na gaba, majiyoyi da dama na kusa da tsohon maitaimakin gwamnan sun bayyana cewa ya gana da tsohon gwamnan jihar, wato Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a gidansa da ke Miller Road a daren Litinin wayewar Talata.
A wata sanarwa da aka fitar a daren jiya Litinin, an ce Gawuna zai yanki katin zama ɗan jam’iyyar ADC a yau Talata a mazaɓarsa ta Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nassarawa.
Sanarwar ta ce, za a haɗu a ƙofar gidan Kwankwaso na Miller Road sannan a garzaya zuwa mazaɓar ta Gawuna domin yankar katin da misalin ƙarfe 11 na safe, kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.
