
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 3 ga watan Afrilu, 2026 da Litinin, 6 ga Afrilu, 2026 a matsayin ranakun hutun bukukuwan ‘Good Friday’ da ‘Easter Monday’.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya yi fatan alheri ga Kiristocin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.
Ya kuma jaddada muhimmancin ɗabi’u masu kyau da sadaukarwa da yafiya da juriya, da haɗin kai da wannan lokaci ke buƙata.
Ya ce, Gwamnatin Tarayya na cigaba da aiwatar da manufofi masu nufin ci-gaban ƙasa, haɗin kai, da arziƙi ga kowa a faɗin Nijeriya.
A cewar sanarwar, hutun ya bai wa Kiristoci damar gudanar da bukukuwan Easter cikin kwanciyar hankali da walwala tare da iyalansu da sauran al’umma.
Gwamnatin ta kuma yi kira ga ‘yan ƙasa da su yi amfani da wannan lokaci wajen ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da kuma addu’o’i domin ci-gaban ƙasa da samun zaman lafiya mai ɗorewa.
