Jagororin APC sun gana da Gwamnan Bauchi yayin da yake shirin koma wa ADC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda tare da tawagarsa suka kai wa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ziyara ta musamman domin lallashinsa ya koma jam’iyyar mai mulki.

A ziyarar, ya karɓi baƙuncin Farfesa Yilwatda tare da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da sauran jiga-jigan APC a ciki da wajen Bauchi.

Hakan na zuwa ne bayan da Gwamna Bala ya gana da tawagar jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal don shiga jam’iyyar.

Da yake ganawa da manema labarai, Gwamnan ya bayyana cewa zai fito da matsayinsa na ƙarshe ga jama’a a ranar Alhamis, 2 ga Afrilu, 2026.

A yanzu dai al’umma na cigaba da jiran wannan muhimmin matsaya da zai iya sauya taswirar siyasa jihar duba da yadda ‘yan siyasa ke sauye-sauyen jam’iyyu yayin da ake ƙara tunkarar babban zaɓen 2027.

By Babaji