
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Alhamis ne Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya bayyana cewa zai koma jam’iyyar adawa ta ADC a wani yanayi mai ɗaukar hankali a fagen siyasa Nijeriya.
A cewar wasu majiyoyi, a yau ne ake sa ran gwamnan zai karɓi bakuncin manyan jami’an ADC a fadar gwamnatin jihar da ke garin Bauchi.
Taron da ake sa ran na zuwa ne a dai dai lokacin da alamu ke nuna cewa ya kammala tuntuɓa da shawarwari dangane da yunƙurinsa na siyasa na gaba.
Masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin cewa idan har aka tabbatar da wannan sauya mataki na iya haifar da gagarumin sauyi a fagen siyasar Bauchi da ma Nijeriya baki ɗaya ganin yadda ake ƙara kusanto babban zaɓen 2027.
Saidai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnan ko ofishinsa da ke tabbatar da faruwar lamarin.
