Kotu ta ƙi dakatar da Sanata Kingibe daga harkokin ADC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA NUHAMMAD

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Abuja ta yi watsi da buƙatar da aka gabatar domin hana Sanata Ireti Kingibe shiga harkokin jam’iyyar ADC, bayan zargin dakatar da ita daga jam’iyyar.

Mai shari’a Peter Lifu ya yanke wannan hukunci a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa ba za a iya amincewa da irin wannan buƙata ba tare da an bai wa wadda ake ƙara damar kare kanta ba.

Shugabannin mazaɓar Wuse, waɗanda rahotanni ke cewa suna da alaƙa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, sun buƙaci kotun da ta bayar da umarnin wucin gadi domin hana Sanata Kingibe bayyana kanta a matsayin ‘yar jam’iyyar ko shiga ayyukanta.

Sai dai mai shari’a Lifu ya jaddada cewa irin wannan mataki yana buƙatar kulawa ta musamman, inda ya ce adalci na buƙatar a bai wa wanda ake tuhuma damar yin bayani kan zarge-zargen da ake yi masa.

Bisa haka, kotun ta umurci a miƙa dukkan takardun ƙarar ga Sanata Kingibe domin ta samu damar shirya kariyarta a gaban kotu.

An shigar da ƙarar ne daga hannun Okezuo Godfrey Anayo da Isaiah Ojonugwa Samuel, a madadin ‘yan kwamitin zartarwa na mazaɓar Wuse, waɗanda suka ce an dakatar da Sanatar tun ranar 10 ga Maris, 2026, bisa zargin aikata ayyukan da suka saɓa da manufofin jam’iyya da kuma rashin ɗa’a.

Sun kuma zargi Sanatar da yin watsi da kundin tsarin jam’iyya tare da tsoma baki a harkokin gudanar da mazaɓa duk da dakatarwar da aka yi mata.

A gefe guda kuma, lauyan da ake cewa yana wakiltar Sanata Kingibe ya sanar da kotu cewa sun riga sun gabatar da wata buƙatar farko da ke ƙalubalantar wannan ƙara.

Daga bisani, kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 20 ga Afrilu, 2026, domin ci gaba da sauraron dukkan buƙatun da ke gaban ta.

By ukarofi