Kira ga tsige Farfesa Amupitan cin fuska ne ga dimukraɗiyya – INEC ga ADC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi tir da kiraye-kirayen tsige Shugabanta Farfesa Joash O. Amupitan, tana mai tirjewa akan hakan ya saɓa wa dokar ƙasa kuma barazana ce ga ‘yan zaman kan tsarin zaɓen Nijeriya.

A wata sanarwa da ta fitar a daren Juma’a a Abuja, hukumar ta ce sukar da wasu ‘yan siyasa ke mata da zargin ta akan zama ‘yar wata jam’iyya ba daidai ba ne, tana mai cewa dukkan ayyukanta suna bisa doka da tsarin shari’a.

INEC ta bayyana cewa batutuwan da suka shafi naɗi, wa’adi da tsige shugaba da kwamishinoninta na jihohi na ƙunshe a fayyace cikin sashe ma 157 na kundin dokar ƙasa na 1999, don haka babu wani ko wata ƙungiyar siyasa da take da ikon neman a tsige shugaban ba tare bin hukuncin doka ba.

A cewarta, ayyukanta na kwanan nan da suka haddasa faɗi-in-faɗa, an gina su ne a ƙarƙashin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara dangane da rikicin shugabanci na cikin gida a jam’iyyar adawa ta ADC.

Ta ce ta yi haka ne domin kauce wa hargitsa tsarin shari’ar kamar yadda ya faru a jihohin Zamfara da Filato, inda aka soke sakamakon zaɓuka saboda saɓa wa umarnin kotu.

INEC ta ƙara da cewa cigaba da sanya ido akan harkokin wani tsagi na ADC musamman jagorancin David Mark, zai kai ga saɓa wa umarnin kotu domin akwai umarnin na musamman daga kotu da ya hana ta haka.

Da take tsokaci akan zargin ta da zama ‘yar amashin shatar gwamnati da ake amfani da ita wajen durƙusar da jam’iyyun adawa, hukumar ta ce har yanzu tana bisa tsarinta na zama a gefe wajen gudanar da harkokin siyasa ba shiga gasar jam’iyya ba.

By Babaji