Sojoji sun jibge tankokin yaƙi a hedikwatar INEC yayin zanga-zangar ADC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An shiga wani yanayi na fargaba da tashin hankali a Babban Birnin Tarayya Abuja, yayin da sojoji da jami’an ’yan sanda masu ɗauke da manyan makamai suka mamaye hedikwatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) a ranar Alhamis, sakamakon barazanar gudanar da gagarumar zanga-zanga daga jam’iyyar ADC.

Rahotanni da hotuna da bidiyoyi da suka bazu a kafafen sada zumunta sun nuna yadda jami’an sojoji da ’yan sanda suka jibge a harabar hukumar, tare da tankokin yaƙi da manyan makamai domin tabbatar da tsaro a yankin.

Wannan mataki na tsaurara tsaro ya biyo bayan rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar ADC, wanda ya raba shugabanninta gida biyu, lamarin da ke ƙara dagula al’amura a siyasar jam’iyyar.

Rikicin ya ƙara tsananta ne bayan da INEC ta sanar a ranar Laraba cewa ta cire sunayen wasu jiga-jigan jam’iyyar daga tsarin rajistarta na yanar gizo.

Daga cikin waɗanda aka cire akwai tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Daɓid Mark, da kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, waɗanda ke riƙe da muƙaman shugaban jam’iyya da sakatare.

Hukumar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne bisa umarnin kotu, inda Kotun ɗaukaka ƙara ta buƙaci a ci gaba da bin halin da ake ciki har sai Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin jam’iyyar.

Rahotanni sun kuma nuna cewa fiye da mutane dubu biyu sun taru a yankin Maitama, kusa da hedikwatar INEC, domin nuna fushinsu kan matakin da aka ɗauka. Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun fito ne daga ADC da kuma ƙungiyar Obidient Moɓement, inda suka shirya zanga-zangar da suka sanya wa suna “Occupy INEC”.

A yayin da rikicin ke ƙara rikicewa, INEC ta bayyana cewa ba za ta amince da kowanne ɓangare na jam’iyyar ba har sai kotu ta yanke hukunci na ƙarshe. Haka kuma, ta ce ba za ta karɓi wata takarda ko hulɗa da kowanne ɓangare ba, tare da dakatar da sa ido kan duk wani taro ko babban zaɓe da kowanne ɓangare zai shirya.

Wannan lamari ya janyo zazzafar muhawara da zargi daga wasu ‘yan jam’iyyar, waɗanda ke ganin cewa akwai yiwuwar nuna son kai ko tsoma bakin siyasa a cikin matakin da hukumar zaɓen ta ɗauka.

Masana siyasa na ganin cewa wannan rikici na ADC da kuma matakan tsaro da aka ɗauka a Abuja na iya ƙara dagula yanayin siyasar ƙasar, musamman yayin da ake tunkarar manyan zaɓuɓɓuka a nan gaba.

By ukarofi