2027: Dalilan da suka sa Ministan Wutar Lantarki bai yi murabus ba

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sabbin bayanai sun bayyana cewa Ministan Wutar Lantarki na ƙasa, Adebayo Adelabu, na iya fuskantar ƙalubale a cikin jam’iyyar APC a Jihar Oyo, yayin da ake tunkarar zaɓen gwamna na shekarar 2027.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya tayar da cece-kuce a cikin jam’iyyar, musamman bayan da Adelabu bai yi murabus daga muƙaminsa ba duk da umarnin Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya buƙaci duk masu riƙe da muƙaman gwamnati da ke da burin tsayawa takara su sauka kafin wa’adin da aka gindaya.

Al’amarin ya ɗauki sabon salo bayan da wata takarda da ake kira “jerin haɗin kai” ta fara yawo, wadda ake zargin tana ɗauke da sunayen waɗanda aka fi so su tsaya takara a muƙamai daban-daban a jihar Oyo.

A cikin takardar, an ambaci Sanata Sharafadeen Alli a matsayin wanda jam’iyyar ke marawa baya domin takarar gwamna, yayin da aka bayyana Soji Adedeji a matsayin mataimakinsa. Haka kuma, an ambaci sunayen Aderemi Oseni da Yunus Akintunde domin kujerun Majalisar Tarayya.

Sai dai, reshen jam’iyyar APC a jihar Oyo ya yi gaggawar ƙaryata takardar, yana mai cewa ƙarya ce kuma an ƙirƙire ta ne domin tayar da rikici a cikin jam’iyyar.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar, Olawale Sadare, ya jaddada cewa har yanzu ba a fara tsarin zaɓen ‘yan takara ba, ciki har da bayyana sha’awa da gudanar da zaɓen fidda gwani.

Duk da wannan ƙaryatawa, wasu na cikin jam’iyyar na ganin fitowar irin wannan jerin na iya nuna cewa ana gudanar da tattaunawa a ɓoye domin cimma matsaya kan ‹yan takara, wata dabara da aka saba gani a siyasar cikin gida ta jam’iyyun Nijeriya.

A baya, Adelabu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a watan Oktoban 2025, yana mai nuna kwarin gwiwa kan samun nasara.

Amma sabbin sauye-sauyen da ke faruwa a cikin jam’iyyar na nuna cewa tasirinsa na siyasa na iya raguwa.

Wani masani a fannin siyasa, Jackson Lekan Ojo, ya nuna cewa rashin gamsuwa daga wasu manyan ‘yan jam’iyyar kan yadda Adelabu ke gudanar da aikinsa a matsayin Ministan Wutar Lantarki na iya shafar matsayinsa.

Har ila yau, wasu majiyoyi sun bayyana cewa a wani taro na musamman da aka yi tsakanin Shugaba Tinubu da wasu gwamnoni a Legas, an tattauna batutuwan tsaro da kuma shirye-shiryen siyasa na gaba, inda rahotanni ke nuni da cewa Adelabu bai samu goyon baya sosai ba.

Duk da cewa wasu ministoci da ke da burin tsayawa takara sun bi umarnin shugaban ƙasa ta hanyar yin murabus, Adelabu ya ci gaba da zama a muƙaminsa, lamarin da ya ƙara jawo jita-jita kan makomarsa a siyasa.

Mai magana da yawunsa, Bolaji Tunji, ya bayyana cewa ministan ba shi da niyyar yin murabus, yana mai ƙaryata rahotannin da ke cewa zai sauka daga muƙaminsa.

Sai dai, wasu majiyoyi masu ƙarfi a cikin jam’iyyar na ganin cewa sauye-sauyen siyasa da ake yi na iya sa Adelabu ya rasa tasirinsa yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

A gefe guda kuma, an ruwaito cewa wasu ministoci uku sun riga sun yi murabus daga Majalisar Zartarwa ta Tarayya domin tsayawa takara, ciki har da Saidu Ahmed Alkali, Yusuf Maitama Tuggar, da Yusuf Sununu.

By ukarofi