Dan hidimar ƙasa, Abba Musa ya samu ’yanci bayan wata uku hannun ’yan bindiga

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani ɗan hidimar ƙasa, wato NYSC, Abba Musa, ya samu ’yancinsa bayan shafe watanni uku yana tsare a hannun ’yan bindiga, lamarin da ya kawo ƙarshen damuwa da fargabar da ta dabaibaye iyalansa da al’umma baki ɗaya.

Rahotanni sun nuna cewa an sako Musa ne a ranar Laraba bayan dogon tattaunawa da matsin lamba daga ’yan Nijeriya da dama da suka bi diddigin lamarin tun daga ranar da aka sace shi. 

Fitowarsa daga hannun masu garkuwa da mutane ta jawo farin ciki ga waɗanda suka daɗe suna addu’ar ganin ya dawo lafiya.

A cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, an ga fitaccen mai wallafa labarai, D English Alhaji, yana tattaunawa da Musa jim kaɗan bayan an sake shi. A cikin bidiyon, Musa ya bayyana godiyarsa ga ’yan Nijeriya bisa addu’o’i, kulawa da goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake cikin wahala.

Abba Musa, wanda ya kammala karatu a Jam’ar Tarayya ta Gusau a fannin Kimiyyar Tsirrai da Fasahar Halittu, an sace shi ne a ranar 9 ga Janairu, 2026, yayin da yake kan hanyarsa daga Gusau zuwa Sakkwato. Sace shi ya sake jaddada damuwa kan tsaron masu yi wa ƙasa hidima, musamman a yankunan da matsalar tsaro ta yi ƙamari.

A lokacin da yake tsare, Musa ya fuskanci tsananin azaba daga hannun ’yan bindigar. Wani bidiyo mai tayar da hankali ya nuna yadda ake dukansa, ana cin zarafinsa tare da tilasta masa roƙon taimako cikin halin azaba. Duk da kukan da yake yi yana neman a taimaka masa, ’yan bindigar sun ci gaba da wulaƙanta shi ba tare da jin tausayinsa ba.

Rahotanni sun ce har ma an taɓa yaɗa jita-jitar cewa ya rasu bayan an biya kuɗin fansa, amma daga bisani ya fito a wani bidiyo yana ƙaryata wannan labari tare da sake roƙon taimakon jama’a domin ganin an kuɓutar da shi.

Sakin nasa ya sake janyo hankali kan yadda matsalar garkuwa da mutane ke ci gaba da addabar arewacin Nijeriya, inda ɗalibai, matafiya da matasa masu yi wa ƙasa hidima ke zama manyan waɗanda ake kai wa hari domin neman kuɗin fansa.

Lamarin Abba Musa ya zama wani darasi mai muhimmanci kan buƙatar ƙarfafa tsaro da kare rayuka, tare da nuna muhimmancin haɗin kai da goyon bayan al’umma wajen tunkarar irin waɗannan matsaloli.

By ukarofi