Daga GAMBO ISA a Abuja
Shugaban ƙungiyar Al’ummar Borno a Arewa maso Gabas (BOCN), Alhaji Bulama Hassan, ya yaba wa Sarkin Biu, Alhaji Dakta Mustapha Umar Mustapha na II, bisa kyakkyawan jagorancinsa da kuma rawar da yake takawa irin ta uba wajen bunƙasa ci gaban masarautar Biu a Jihar Borno.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma aka rabawa jaridar Blueprint a Abuja, Bulama Hassan ya bayyana hakan ne yayin bikin naɗa rawani ga ɗiyar masarautar, Hajiya Larai Umar Mustapha, wadda ita ce Babbar Sakatariya ta ƙaramar hukumar Kwaya Kusar. An naɗa ta da sarautar “Majira ta Biu” tare da zama mai bai wa majalisar masarautar shawara.
Ya kuma yi kira ga Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da ya ci gaba da tallafa wa ci gaban masarautar Biu, musamman a fannin noma da kiwon dabbobi.
Bulama Hassan ya ƙara da roƙon gwamnan da ya tallafa wajen kammala aikin Dam ɗin Biu, wanda ya shafi ƙananan hukumomi huɗu — Biu, Kwaya Kusar, Hawul da Bayo — yana mai cewa kammaluwar aikin zai ƙara bunƙasa samar da abinci a yankin da ma jihar baki ɗaya.
Ya bayyana Biu a matsayin muhimmin cibiyar noma kuma rumbun abinci a Arewa maso Gabas, inda ya buƙaci gwamnatin jiha da Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas (NEDC) da su ba da fifiko wajen kammala aikin dam ɗin.
A cewarsa, kammala Dam ɗin Biu ba kawai zai inganta noma ba ne, har ma zai samar da ayyukan yi ga matasa a faɗin masarautar.
Shugaban na BOCNE ya kuma yaba wa Sarkin Biu bisa yadda yake tabbatar da zaman lafiya da tsaro a masarautarsa tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da gwamnatin jiha.
Haka kuma, ya yabawa Sarkin bisa naɗa Hajiya Larai Umar Mustapha a matsayin Majira ta Biu tare da ba ta matsayin mai ba da shawara ga majalisar masarauta, yana mai cewa wannan mataki yana ƙarfafa haɗin kai da ci gaba.
Bulama Hassan ya buƙaci matasa da dattawan masarautar da su mara wa shirye-shiryen gwamnati baya, musamman a fannin noma da kiwon dabbobi, tare da zama jakadu nagari na masarautar Biu da Jihar Borno gaba ɗaya.
A ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar yankin ba tare da la’akari da bambancin addini ba da su haɗa kai wajen tallafa wa shirye-shiryen gwamnati, su zauna lafiya, su kuma guji shaye-shayen miyagun ƙwayoyi domin gina masarauta, jiha da ƙasa mai ƙarfi.
