FIFA na neman faɗaɗa adadin ƙasashen gasar Kofin Duniya zuwa 64

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da harkokin ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA) ta tabbatar da cewa ta fara aikin faɗaɗa adadin ƙasashen da za su fafata a gasar Kofin Duniya na 2030 zuwa 64 domin ƙara wa gasar armashi.

A cewar The York Times, Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa na ƙasar Uruguay, Ignacio Alonso ne ya gabatar da shawarar a karom fari a Maris ɗin shekarar 2025.

Shugaban FIFA Gianni Infantino ya bayyana shawarar da matsayin abin da ke buƙatar a yi wa karatun ta nitsu da sharhi mai faɗi.

Matuƙar aka amince da wannan shawara, ƙasashen da za su riƙa fafatawa a gasar za su ƙaru daga 48 da aka tsara a na 2026 zuwa 64.

Lamarin da zai ninka adadin wasannin daga na ƙasashe 32 zuwa guda 128.

Tuni dai aka samu ƙwararru a fannin ƙwallon ƙafa na sukar shirin ganin yadda zai iya haifar da tsaiko da kalandar wasannin matakin ƙasa-da-ƙasa.

By Babaji