
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar adawa ta ADC ta tirje akan cigaba da shirinta na gudanar da babban taro da wasu taruka duk da cewa Hukumar Zaɓe (INEC) ta ƙi amince wa shugabancinta.
A wata sanarwa da Sakataren Shirye-shiryenta na Ƙasa, Bolaji Abdullahi ya fita a yau Juma’a, ADC ta ce za gudanar da tarukan nata daga ranar 7 zuwa 14 ga watan nan na Afrilu, 2026.
Ya ce, za a fara ne da tantance ‘yan takara sannan a kammala da babban taro na ƙasa.
Don haka ne ta sanar da ɗaukacin mambobinta duk da gargaɗin INEC akan aiwatar da haramtattun ayyuka. Jam’iyyar ta sanar da INEC ta wasiƙu masu ɗauke da kwanan watan 27 ga Fabrairu, 2026 da kuma 28 ga Maris, 2026.
Ga wani sashe na wasiƙar kamar yadda IntelRegion ta ruwaito: “Screening of Aspirants—7th April 2026; Appeals on Screening Exercise—8th April 2026; Polling Unit, Ward, and Local Government Congresses – 9th April 2026; Appeals on the Congresses-10th April 2026; State Congresses-11th April 2026; Appeals on the State Congresses-12th April 2026 and Convention-14th2026; April 2026.”
Wannan sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin shugabanci ya hi zurfi acikin jam’iyyar bayan INEC ta ƙi aminta ko tabbatar da shugabancin tsagin su David Mark da Rauf Aregbesola a farkon makon nan.
