Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Matar Gwamnan Jihar Zamfara, Mai martaba, Huriyya Dauda Lawal, ta halarci wani babban taron masu ruwa da tsaki a Ffadar shugaban ƙasa, Abuja, inda aka yi bikin rantsar da kwamitin amintattu da kuma ƙaddamar da asusun amincewa na bankin abinci na ƙasa a hukumance.
Jawabin hakan na ƙunshe a wata sanarwa da sakatariyar yaɗa labarai a ofishin matar gwamnan Rabi Yusuf ta rabawa manema labarai yau Juma’a a Gusau.
Shirin, wanda uwargidan shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta jagoranta, yana wakiltar wani shiri na ƙasa da ƙasa kan matsalar rashin abinci da kuma jajircewa wajen inganta samun abinci mai gina jiki ga al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali a faɗin ƙasar.
A lokacin da take jawabi a wurin taron, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bayyana shirin a matsayin wanda ya dace, duba da halin da ake ciki a yanzu na zamantakewa da tattalin arziki da gidaje da dama na Najeriya ke fuskanta.
Ta lura cewa shirin ya wuce magance yunwa, tana mai jaddada rawar da ake takawa wajen dawo da mutunci da kuma ƙarfafa al’ummar ƙasar nan ta hanyar tsarin da zai ɗore.
Uwargidan Gwamnan Zamfara ta ƙara jaddada cewa manufofin asusun tallafawa sun yi daidai da muhimman abubuwan da Gwamnatin Jihar Zamfara ta sa a gaba na ci gaba, musamman wajen ƙarfafa tsarin abinci na gida, ƙarfafa manoma masu ƙananan gonaki da kuma inganta samar da isashshen abinci mai gina jiki ga mata da yara.
Ta bayyana ƙwarin gwiwa kan yiwuwar wannan shiri na samar da sauye-sauye masu ma’ana ga jama’a ta hanyar haɗin gwiwa na dabarun wayar da kan jama’a da kuma shirye-shiryen da aka tsara don rage rashin abinci mai gina jiki.
Ta kuma yaba da hangen nesa, jagoranci da jajircewar waɗanda suka shirya taron, tana mai sake tabbatar da shirye-shiryen Jihar Zamfara na yin aiki tare, ɗaukar mafi kyawun ayyuka da kuma faɗaɗa shirye-shiryen ƙirƙire-ƙirƙire waɗanda ke samar da fa’idodi masu ɗorewa ga zamantakewa da tattalin arziki ga jama’ar jihar.
