Tashin jirgi da dare bai dace da yanayi mai kyau ba – Fadar Shugaban Ƙasa kan ganawar Tinubu da ‘yan Filato a ‘yan mintuna

Spread the love

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana dalilan da suka sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya gana da waɗanda hare-haren jihar Filato ya shafa a filin jirgin sama maimakon shiga cikin garin Jos.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce jadawalin shugaban ƙasa na ranar Alhamis ya haɗa da manyan ayyuka biyu; karɓar baƙuncin shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno, da kuma tafiya zuwa Iperu a Jihar Ogun.

Sanarwar ta ce bayan samun bayani daga gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, shugaban ƙasa ya dakatar da shirinsa na tafiya Ogun domin mayar da hankali kan halin da ake ciki a Jos. Sai dai ba zai yiwu ya dage ganawar da shugaban ƙasar Chadi ba, wadda aka bayyana a matsayin mai muhimmanci wajen ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

An ƙara da cewa ganawar ta ɗauki lokaci fiye da yadda aka tsara, lamarin da ya jinkirta tashin shugaban ƙasa zuwa Jos.

Da isowarsa Jos kuwa, sanarwar ta ce an fuskanci ƙalubalen sufuri, inda aka bayyana cewa filin jirgin saman bai da kayan aikin da ke ba da damar saukar jirage da dare.

Haka kuma nisan tafiya daga filin jirgin zuwa cikin birnin Jos na ɗaukar kusan mintuna 40, abin da ya sa ya zama da wahala shugaban ƙasa ya shiga cikin gari ya gana da waɗanda abin ya shafa sannan ya koma filin jirgin kafin duhu.

Saboda haka ne jami’an gwamnatin jiha da na tarayya suka yanke shawarar kawo wakilan al’ummomin da abin ya shafa zuwa wani ɗaki kusa da filin jirgin sama domin shugaban ƙasa ya gana da su cikin gaggawa ba tare da karya dokokin tashi da saukar jirage ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa a cikin waɗanda suka halarci ganawar akwai Ministan Tsaro, Babban Hafsan Sojojin Ƙasa da kuma Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, waɗanda tuni suka kai ziyara zuwa Rukuba, inda aka fi samun tasirin rikicin.

Haka kuma shugaban ƙasa ya tura wata babbar tawaga zuwa yankin, ciki har da mai taimaka masa kan hulɗa da al’umma, domin gudanar da muhimman ayyuka na tsaro da sasanta al’umma kafin zuwansa.

Fadar Shugaban Ƙasa ta jaddada cewa matakan da aka ɗauka sun kasance domin tabbatar da saurin kai ɗauki da kuma kiyaye tsaron tafiyar shugaban ƙasa a lokaci guda.

By Babaji