Koma wa dimukraɗiyya tamkar dawo da mulkin mallaka ne – Shugaba Traore ga ‘yan Burkina Faso

Spread the love

Shugaban gwamnatin mulkin soja ta ƙasar Burkina Faso, Ibrahim Traoré, ya bayyana cewa tsarin dimokuraɗiyya irin na ƙasashen Yamma bai dace da ƙasarsa ba, yana mai danganta shi da wani nau’in bautar zamani.

Traoré ya yi wannan furuci ne a wata hira da ya bayar a daren Alhamis, yayin da ake cika shekara guda da ƙaddamar da wata manufa mai taken Juyin Juya Halin Ci gaban Jama’a (RPP), wadda ya ƙirƙira a watan Afrilun bara.

A cewarsa, manufar RPP an gina ta ne domin tabbatar da cikakken ‘yancin kai na ƙasa da kuma bunƙasa tattalin arziki mai dogaro da kai, ta hanyar kawar da duk wani tasiri na waje, musamman abin da ya shafi tsohon tsarin mulkin mallaka.

Ya ƙara da cewa tsarin dimokuraɗiyya na Yamma ba shi ne mafita ga ƙasashen Afirka ba, yana mai cewa ya kamata a maye gurbinsa da tsare-tsaren juyin juya hali da za su ba ƙasashe damar cimma cikakken ‘yanci da ci gaba.

Kalaman nasa na ƙara jawo muhawara a tsakanin masana da ‘yan siyasa, musamman kan dacewar tsarin dimokuraɗiyya a nahiyar Afirka da kuma hanyoyin da za su kai ga ci gaba mai ɗorewa.

By Babaji