Daga USMAN KAROFI
Babban mataimaki na musamman ga Shugaban ƙasa kan harkokin sarauta, Abbas Tijjani Hashim, ya sanar da ƙaddamar da wani sabon tsarin sa-ido da tantance ayyuka da nufin bunƙasa al’adun gargajiya tare da tallafa wa shirye-shiryen gwamnati a matakin ƙananan hukumomi.
Alhaji Abbas Tijjani Hashim, wanda kuma ke riƙe da sarautar Sarkin Sudan na Kano, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manyan masu riƙe da sarautu, ciki har da sabon Sarkin Yamma na Bwari, Alhassan Musa Baba Chukuri, da Dan Galadiman Kwangwami, Lauwali Ibrahim.
A cewarsa, wannan shiri ya yi daidai da manufar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ƙarfafa cibiyoyin gargajiya da tabbatar da cewa al’adu suna bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban ƙasa. Ya ƙara da cewa tsarin zai taimaka wajen bibiyar da kuma tantance tasirin shirye-shiryen al’adu da na al’umma a faɗin Najeriya.
A yayin taron, an tattauna kan muhimmiyar rawar da shugabannin gargajiya ke takawa wajen kare al’adu, ƙarfafa haɗin kai, da kuma bunƙasa shiga harkokin ƙasa daga ɓangaren jama’a. Mahalarta taron sun jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da sarakuna domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
Haka kuma, Abbas Tijjani Hashim ya buƙaci sarakunan gargajiya a faɗin ƙasar nan da su kasance masu lura tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankunansu. Ya ce rawar da suke takawa na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da kwanciyar hankali a matakin ƙasa.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin da gwamnatin Tinubu ke yi na haɗa al’adun gargajiya cikin tafiyar da mulki tare da ƙarfafa tsarin al’umma a faɗin Najeriya.
