Likitoci sun fara yajin aiki a yau kan bashin da suke bi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yajin aikin da Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Ƙasa (NARD) ta sanar da farawa ka iya jefa fannin lafiya a Nijeriya cikin mawuyacin hali a matakin asibitocin jihohi da na ƙasa.

NARD ta ɗauki wannan mataki ne na sai baba-ta-gani a fadin ƙasar sakamakon matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na dakatar da aiwatar da gyaran fuska na alawus-alawus na ƙwararrunta.

Babban sakataren kungiyar, Shuaibu Ibrahim, ne ya bayyana hakan bayan da kungiyar ta gudanar da wani taron majalisar zartarwar ta a ranar Asabar.

Ya bayyana cewa, yajin aikin zai fara ne da misalin ƙarfe 12:00 na safiyar ranar Talata 7 ga watan Afrilu.

Sakataren ya bayyana takaicinsa akan matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na dakatar da tsarin alawus-alawus ɗin ƙwararrun, inda ya ce hakan zai jefa rayukan marasa lafiya cikin haɗari.

Wannan taƙaddama ta samo asali ne bayan yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayya bayan wani yajin aiki da su ka dauki dogon lokaci su na yi a shekarar 2025.

Daga cikinsu akwai ƙarin kuɗaɗen alawus na zuwa aiki, aikin dare, da kuma alawus ɗin tura likitoci zuwa karkara domin inganta walwalarsu, duk kuwa da cewa an fara aiwatar da tsarin a farkon watan Janairu 2026, daga bisani aka koma gidan jiya a watan Fabrairu.

Akan haka ne ƙungiyar ta zargi Gwamnatin Tarayya da shirin dakatar da biyan kuɗaɗen a watan Afrilun nan, inda Sakataren ya jaddada cewa wajibi ne a biya sauran albashin wasu cibiyoyin lafiya da kuma kuɗaɗen horar da likitoci na shekarar 2026, ba tare da ɓata lokaci ba.

Har ila yau, NARD na neman a biya bashin alawus na kwararru na tsawon watanni 19 da ke hannun gwamnati.

Kazalika ta buƙaci mambobinta a dukkan faɗin jihohin ƙasar nan da su bayar da haɗin kai har zuwa lokacin da za a biya musu buƙatun da suka gabatar wa gwamnatin.

By Babaji