Gwamna Raɗɗa ya bada tallafin Naira miliyan 31 ga al’ummar Sayasa da harin ‘yan bindiga ya shafa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya tallafawa mutanen da hare haren ‘yan bindiga ya shafa a garin Sayaya a ƙaramar hukumar Matazu da Naira miliyan 31.

Da yake miƙa tallafin kuɗin ga mutanen da harin ya shafa , Gwamna Dikko Raɗɗa wanda ya sami wakilcin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Abdulkadir Nasir Andaje ya ce ba wai ƙudirin gwamnati na kare rayuka da dukiyar al’umma ba har da taimakawa mutanen da hare haren ya shafa domin rage raɗaɗi.

Andaje ya bayyana cewa Gwamna Raɗɗa ya sami bayanin hare haren ‘yan bindiga a yankin bayan dawowarsa daga ƙasar China.

“Duk da matsalar tsaro, gwamna ya ce sai ya je Sayaya,hakan ya nuna yadda gwamnan ke tare da al’ummar sa,”inji Andaje.

“Malam Dikko Raɗɗa ya na tare da ku a cikin wannan halin na alhini wanda haka ya bada umurni a gaggauta bada wannan tallafi domin sake gina rayuwa,”Andaje ya ce.

Ya tabbatar wa al’ummar garin cewa gwamnati za ta yi bakin ƙoƙarin ta na ganin irin wannan ɓarna babta sake faruwa ba. Kan hake ne gwamna ya bada umurnin ƙara kawo jami’an tsaro a yankin.

Naira miliyan 21 cikin kudin za a rabawa mutane 51 da rikicin ya shafa,sai waɗanda aka kona motocin su zasu sami Naira miliyan biyu.

Sauran kuɗin za a rabawa waɗanda aka ƙona shagunan su da sauran asarar da suka yi.

Da yake jawabi shugaban ƙaramar hukumar Matazu Alhaji Shamsuddeen Muhammad ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa kan matakin da ya ɗauka na gaggawa wajen tallafa wa mutanen da hare haren ya shafa.

By ukarofi