ADC: Atiku, Obi da Kwankwaso sun shiga sahun masu yi wa INEC zanga-zanga a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma Peter Obi sun jagoranci gagarumar zanga-zanga zuwa ofishin INEC a Abuja a yau Laraba.

Rahotanni sun ce zanga-zangar ta haɗa da manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC, ciki har da Rauf Aregbesola, Aminu Waziri Tambuwal, Dino Melaye da David Mark.

Zanga-zangar na zuwa ne bayan zargin da jam’iyyar ADC ta yi cewa INEC tana goyon bayan jam’iyyar APC domin hana ta damar tsayar da ‘yan takara a zaɓen 2027. Amma INEC ta musanta zargin, inda ta ce tana aiki ne bisa doka da umarnin kotu.

Rikicin cikin gida na ADC ya ƙara ƙamari ne bayan da INEC ta cire sunayen David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakatare daga tsarinta na yanar gizo.

Rahotanni sun nuna cewa ana cigaba da taƙaddama tsakanin Nafiu Bala da David Mark kan shugabancin jam’iyyar, lamarin da ya kai ga shari’a a kotu.

Haka kuma, INEC ta ce za ta cigaba da bin umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara wajen magance rikicin shugabanci da ke cigaba da addabar ADC.

By Babaji