Dalilin da ya sa na sake barin APC zuwa PDP – Dakta Umbugadu

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Keffi

Ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa Dr, David Ombugadu yace ya sake barin jam’iyyar APC mai ci a jihar Nasarawa cikin makonni ƙalilan da shigawarsa ne saboda gazawar jam’iyyar APC ɗin wajen yi wa al’ummarsa rajista da kuma yinƙurin daƙile masa burinsa na zama gwamnan jihar a 2027.

Hon. Dr. Ombugadu wanda ya tsaya takarar gwamna a jihar ta Nasarawa a shekarar 2019 da 2023 a tikitin PDP ya bayyana haka ne a yayin wata ziyarar da yayi na musamman kai tsaye zuwa ofishin mambobin ƙungiyar ‘yan jaridu ta Correspondents’ Chapel na Nigeria Union of Journalists (NUJ) dake Lafia.

Yace shigarsa APC ba domin mai da wani shugaban jam’iyyar ko nemo wa wani mukami ba ne, amma maimakon a ba kowa damar yin rajistar zama ɗan jam’iyyar na asali amma sai ake yi wa wasu ana hana mutanensa damar.

Yace a yanzu haka ya sake komawa PDP tare da sanar da cewa zai sake tsayawa takarar gwamna a 2027 a tikitin PDP ɗin.

Ya cigaba da bayyana cewa “Na dawo PDP muna tare da mutane na kuma tuni na ɗauri ɗamarar yi musu bauta da zarar Allah ya bani nasarar.

Dr. Umbugadu ya kuma yi amfani da damar inda ya sanar cewa tabbas duk da a yanzu yana PDP amma zai yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu hidima don tabbatar da nasarar sa a 2027 saboda gagaruman sabbin ayyukan cigaba da Bola Tunubu yake gabatarwa a ƙasar nan baki ɗaya kawo yanzu.

Yace ziyarar nasa da tawagarsa zuwa ofishin Correspondent chapel ɗin naɗa manufar ƙarfafa neman alaƙa ne da kuma buƙatar goyon bayan su.

Tun farko a jawabin shugaban ƙungiyar masu aiko da labarin ta Correspondent Chapel reshin jihar Nasarawa Kwamaret Abubakar Abdullahi ya marabci ɗan takarar zuwa ofishin inda ya tabbatar masa cewa a shirye ƙungiyar take tayi aiki da duka ‘yan takara a jihar baki ɗaya.

By ukarofi