Daga HABU ƊAN SARKI a Jos
A wani mataki na musamman da nufin kawo sauyi a siyasar Jihar Filato da kuma biyayya ga umarnin jagoransa na siyasa, madugun ɗariƙar Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya a Filato Muhammad Shafi’u Yakubu Sahlan tare da dubban magoya bayansa sun yi canjin sheƙa daga Jam’iyyar NNPP zuwa ADC.
Sanata Shafiu Sahlan, wanda ya zo na biyu a zaɓen kujerar Sanata mai wakiltar Shiyyar Filato ta Arewa a babban zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, ya karɓi katin shaidar zama ɗan jam’iyyar ADC ne a reshen mazaɓarsa ta unguwar Naraguta B. yayin wani gagarumin taron karɓar sabbin ƴan Jam’iyya da aka gudanar bisa jagorancin shugabar jam’iyyar ADC a Jihar Filato, Hannatu Gagara.
Sahlan wanda ake yi masa laƙabi da baya mai goya marayu, kuma jagoran aƙidar siyasar kawo canji ta Sahlaniyya, ya ce ya yi wannan canjin sheƙa ne domin koyi da jagoransa kuma madugun Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda shi ne ya fara jagorantar wannan sauyi zuwa jam’iyyar ADC, domin gina sabuwar Nijeriya bisa tsari da manufofin da suka dace da aƙidar Kwankwasiyya.
Shafi’u Sahlan ya yi godiya ga shugabannin jam’iyyar ADC a Jihar Filato da suka karɓe shi da magoya bayansa zuwa cikin jam’iyyar su, tare da bayyana cewa shigar ƴan Kwankwasiyya zuwa jam’iyyar ADC tamkar gobara ce daga kogi, kamar yadda ake gani tun bayan da Sanata Kwankwaso ya ayyana komawarsa cikinta.
Ya ƙara da cewa shi da ɗimbin magoya bayansa da suka haura dubu 63 za su kawo wa jam’iyyar ADC sabon canji a siyasar Jihar Filato, tare da fatan ba za a nuna musu wariya ba, kuma za a ja mabiyansa a jiki, domin ba su dama cikin jam’iyyar don su ma su ba da tasu gudunmawar. Yayin da ya ƙara kira ga mabiyansa da su tabbatar sun yi rijistar katin zaɓe, kuma su sabunta katinsu don samun damar yin zaɓen shugabanni nagari a Babban Zaɓe mai zuwa na 2027.
A jawabinta na maraba, shugabar jam’iyyar ADC a Jihar Filato Hon. Hannatu Gagara ta bayyana matuƙar farin cikinta da samun waɗannan sabbin mambobi tare da yi wa kowa maraba, kuma ta yi fatan za su zauna da zuciya ɗaya, don yin aiki tare, domin cigaban ADC da Nijeriya bakiɗaya.
Ta nuna cewa, jam’iyyar ADC ta yi tanadi na musamman domin tallafawa rayuwar mata da matasa, da kuma ƙarfafa musu gwiwa su shiga siyasa, domin kawo sauyi a Jihar Filato da Nijeriya baki ɗaya.
Baƙo na musamman a taron, kuma babban mai tsawatarwa na ƙasa a Jam’iyyar ADC, Hon. Sabi’u Musa, wanda tun 2006 ya kai jam’iyyar zuwa Filato, har ta samu kafuwa da magoya baya, ya bayyana cewa tun a shekarar 2015 Jam’iyyar ADC take zawarcin Sanata Kwankwaso don ya zo ya yi mata takara, amma Allah bai nufa ba sai a wannan karon. Ya ƙara ƙarfafa gwiwar ƴan Kwankwasiyya da suka shiga cikin jam’iyyar da su bai wa shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa zuwa jiha goyon baya, da yin aiki tare domin kawo sauyin da ƴan Nijeriya za su amfana.
Taron ya samu sanya albarka daga manyan baƙi da suka halarci bikin shaida karɓar sabbin mambobin ADC, da suka haɗa da jiga-jigan ƴan jam’iyyar da masu yi mata takara irin su shugaban ADC a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, Hon. Ɗanladi Shu’aibu Jibrin, da Hon. Abdulhadi Abdullahi Cokali, Hon. Ado Datti, da Raba Gardama Hon. Jamilu Lawandi Datti, sai kuma Hon. Solomon Nandeng, tsohon ɗan takarar kujerar gwamna a zaɓen 2023.
Gaba ɗayansu sun bayyana yabawa da farin cikinsu da samun ƙarin cincirindon magoya baya, da kuma jinjina ga kyakkyawan jagoranci da aƙida irin ta madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
