Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da kwamitin gudanarwa na bankin Amana Microfinance domin faɗaɗa da kuma inganta ayyukan bankin na gwamnati. An gudanar da bikin ƙaddamarwar a fadar gwamnatin Jihar Katsina, wanda ya yi daidai da manufofin babban bankin Nijeriya (CBN) na bankunan microfinance.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Raɗɗa ya bayyana mambobin kwamitin a matsayin mutane masu gaskiya da ƙwarewa a harkar banki. Ya ce an zaɓe su ne bisa cancanta domin su taimaka wajen tafiyar da bankin yadda ya kamata tare da bunƙasa shi. Ya kuma nuna ƙwarin gwiwarsa cewa za su sauke nauyin da aka ɗora musu yadda ya dace.
Gwamnan ya sanar da naɗin Alhaji Muntaka Badaru Jiƙamshi a matsayin Shugaban Kwamitin, yayin da Manajan Darakta na bankin, Umar Zubairu, zai kasance sakatare. Sauran mambobin sun haɗa da kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Malik Anas; Mohammed Lawal Mukhtar, Dr. Mohammed Bashir Ruwa Godiya; Dr. Bello Mohammed, Alhaji Nasir Mandila Karofi da Hajiya Badiyya Hassan Mashi. Haka kuma, mai bai wa Gwamna Shawara kan harkokin banki da kuɗi, Hajiya Bilkisu Sulaiman Ibrahim, za ta kasance mai lura.
Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta ƙara jarin bankin zuwa kusan naira biliyan ɗaya domin ba shi damar gudanar da cikakken aikin bankin microfinance. Ya bayyana cewa an yi gyare-gyare domin bankin ya biya bukatun kuɗi na cikin gida, musamman ga hukumomin gwamnati da yankunan da ba su da bankunan kasuwanci.
A nasa jawabin karɓar muƙami, Shugaban Kwamitin, Alhaji Muntaka Badaru Jikamshi, ya yabawa gwamnan kan hangen nesa wajen bunƙasa harkokin kasuwanci a jihar. Ya ce za su yi aiki tukuru domin tabbatar da bankin ya cimma manufofinsa domin amfanin al’ummar Jihar Katsina.
