Labarin bogi daga Nijeriya – Trump ya caccaki CNN akan rahoton tsagaita wuta na Iran

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Donald Trump na Amurka ya zargi gidan yaɗa labarai na CNN da wallafa rahoton ƙarya akan tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, inda ya ce rahoton ya samo asali ne daga wani shafin labarai na ƙarya daga Nijeriya.

A cewarsa, CNN ta gina rahoton ne akan bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, tare da kira ga gidan labaran da ya janye rahoton, duk da cewa bai gabatar da wata hujja ko bayyana sunan shafin da yake zargi ba.

Sai dai har yanzu babu wata kafar labarai ta Najeriya da aka tabbatar da ita a matsayin tushen rahoton ko ta yi ikirarin alhaki a kai.

Tuni dai Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce ƙasarsa za ta dakatar da matakan kare kai idan aka daina kai mata hari, yana mai nuni da yiwuwar sassauta rikicin da aka shafe sama da wata guda ana fafatawa.

Duk da cewa Trump ya tirje akan cewa asalin rahoton daga Nijeriya ne da aka yaɗa bisa ƙarya, babu wata kafa daga cikin kafafen yaɗa labarai a Nijeriya da ta tabbatar da ikirarin nasa.

Wannan al’amari ya janyo hankalin duniya akan yadda bayanai ke yaɗuwa cikin sauri ba tare da sahihin tushe ba, tare da jefa fannin yaɗa labaran Nijeriya a tsakiyar muhawara game da sahihancin labaran da ake yaɗawa a ƙarƙashinsa.

By Babaji