
Wasu daga cikin ‘yan kasuwar zamani ta Kabiru Abubakar Bichi, sun koka bisa matsalar rashin samun shagunansu da aka karɓa sakamakon gyara da aka yi a kasuwar a shekarun baya.
Jami’ar Yaɗa Labarai ta Ƙaramar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta rawaito Shugaban ƙungiyar kasuwar, Alhaji Abubakar Mazahimu Sale, ya bayyana ‘yan kasuwar cike suke da buƙatar a raba musu shagunan da aka samu damar ginawa a halin yanzu domin cigaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu yadda yakamata.
“Mun daɗe muna jiran tsammani, a satin da ya wuce kuma, sai ɗanmajalisa ya aiko cewa a sa rana zai zo ya buɗe kasuwar; to ta yaya za a buɗe kasuwa ba tare da an gama aikin gina shaguna an raba wa ‘yan kasuwa ba, kuma ba tare da an yi musu wani bayani gamsasshe ba ta yadda haƙƙinmu zai kasance.
Wannan shi ne abin da ya ja hankalinmu muka kama kiraye-kiraye a yi mana adalci, domin babu yadda za a yi a ce za a buɗe kasuwa ba tare da an kammala shaguna an bai wa ‘yan kasuwa ba. Muna bin shaguna a ƙalla kusan 677 a ce za a buɗe kasuwa, idan an buɗe ina makomar sauran shagunan namu?” Alhaji Abubakar Mazahimu Sale
Bisa haka, Shugaban Kasuwar Zamanin ta Bichi, Alhaji Garba Tukur, da Jami’ar Yaɗa Labaran yankin ta zanta da shi, ya bayyana matsayar haƙiƙanin halin da ake ciki game da tabbatar da haƙƙoƙin ‘yan kasuwar bisa doron adalci.
Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya tabbatar kasuwar an ingantata ne domin cigaba da kuma bunƙasa tattalin arziki domin gogayya da kasuwannin ƙasar Nijeriya.
Akan haka ne kasuwar ta fuskanci yanayin ƙarancin shaguna sakamakon hanyoyi da aka fitar a cikinta.
Ya kuma bayyana cewa a tsaye suke wajen ganin kowa an mayar masa da shagonsa ko shagunansa a cikin lumana.
“Akwai wani fili na tasha da za a yi amfani da shi wanda zai iya ɗaukar adadin rumfunan da ‘yan kasuwar suke buƙata, a yanzu haka akwai guda 400 da aka gama ginawa daga cikin rumfunan 700 da ake yi, waɗanda za mu ƙara ba su wuce 300 da wani abu ba, kuma filin da za a gina sun, an yi tanadinsa yana nan a ƙasa.
A matsayar da ‘yan kasuwar suke ciki dai a wannan gaɓar cewa suka yi, suna nan a kan bakansu na aniyar cigaba da bibiyar haƙƙoƙinsu ta hanyoyin ɗa’a da lumana da kuma fatan hukumomi za su duba wannan batu a cikin gaggawa domin kyautata rayuwar waɗanda abin ya shafa.
