Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil, Neymar, ya fuskanci suka mai tsanani daga jama’a da masoya wasanni bayan furucin da ya yi game da alƙalin wasa bayan kammala wasa tsakanin ƙungiyarsa ta Santos da Remo, wanda ya ƙare da ci 2-0.
Rahotanni sun bayyana cewa Neymar ya nuna rashin jin daɗinsa ga alƙalin wasa, Savio Sampaio, bayan da aka ba shi katin gargaɗi sakamakon ƙorafi da ya yi kan wani mummunan bugun da ɗan wasan hamayya, Diego Hernandez, ya yi masa.
A ƙarshen wasan, Neymar ya yi yunƙurin yaudarar alƙalin wasa yayin bugun freekick, abin da ya sa Hernandez ya yi masa wani ƙarfi daga baya. Bayan hakan ne Neymar ya kai ƙorafi ga alƙalin wasa, amma maimakon a ba shi kariya, sai aka nuna masa katin gargaɗi.
Yayin da yake magana bayan wasan, Neymar ya bayyana cewa ya ji an zalunce shi, yana mai cewa wannan ba shi ne karo na farko da ake masa irin wannan bugun ba. Sai dai furucin da ya jawo cece-kuce shi ne lokacin da ya danganta halin alƙalin wasan da wani maganar da ake ganin ta raina mata, abin da ya janyo suka daga mutane da dama a kafafen sada zumunta.
Bayan wannan lamari, Neymar ya fito ya nemi afuwa, yana mai bayyana nadamarsa kan abin da ya faɗa. Ya amince cewa kalamansa ba su dace ba, musamman ganin yadda suke iya tauye darajar mata a harkar wasanni.
Masana da masu sharhi sun bayyana cewa irin wannan furuci ba ya dacewa daga ɗan wasa mai matsayi da tasiri kamar Neymar, wanda ake kallon sa a matsayin abin koyi ga matasa a duniya.
A gefe guda kuma, har zuwa yanzu hukumomin ƙwallon ƙafa na Brazil ba su sanar da hukuncin da za a ɗauka a kansa ba. Sai dai ana sa ran za a duba lamarin domin tabbatar da ɗabi’a mai kyau a harkar wasanni.
Lamarin ya sake tayar da muhawara kan yadda ya kamata ’yan wasa su riƙa mutunta dokoki da kuma masu gudanar da wasa, tare da kauce wa kalaman da ka iya haifar da rashin daidaito ko cin zarafi.
