FIFA na nazarin faɗaɗa gasar Kofin Duniya zuwa ƙasashe 64 domin bikin cikarta shekara 100

Spread the love

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA), ta tabbatar da cewa tana duba wani shiri da aka gabatar na faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2030 zuwa ƙasashe 64, a wani yunƙuri na bikin cika shekara 100 da fara gasar.

Rahotanni sun nuna cewa wannan ra’ayi ya samo asali ne daga shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Uruguay, Ignacio Alonso, a wani taron majalisar FIFA da aka gudanar a watan Maris na shekarar 2025. Daga bisani, ƙungiyar ƙasashen Kudancin Amurka ta CONMEBOL ta gabatar da wannan shawara a hukumance, inda shugabanta Alejandro Domínguez ya bayyana cewa hakan zai bai wa duk duniya damar shiga cikin bikin, ba tare da barin kowa a baya ba.

Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya bayyana wannan shawara a matsayin abin da ya kamata a yi nazari a kai sosai, yana mai cewa duk wata sabuwar dabara tana da muhimmanci wajen tunawa da cikar shekara 100 da fara gasar Kofin Duniya ta farko da aka yi a Uruguay.

Idan aka amince da wannan tsari, yawan ƙasashen da za su halarci gasar zai ƙaru daga 48 da aka riga aka tsara domin gasar 2026 zuwa 64, abin da zai ninka yawan wasanni zuwa 128, idan aka kwatanta da tsohon tsarin ƙasashe 32.

Sai dai wannan shiri ya fuskanci turjiya daga wasu manyan shugabannin ƙwallon ƙafa na duniya. Shugaban ƙungiyar Turai ta UEFA, Aleksander Ceferin, ya soki wannan ra’ayi, yana mai kiran sa da mummunan tsari. Haka kuma shugaban CONCACAF, Victor Montagliani, ya bayyana cewa bai dace a ƙara faɗaɗa gasar ba kafin a gwada tsarin ƙasashe 48 da za a fara amfani da shi.

A ɓangaren nahiyar Asiya ma, shugaban Asian Football Confederation, Sheikh Salman bin Ibrahim Al Khalifa, ya yi gargadin cewa irin wannan faɗaɗa na iya haddasa ruɗani a jadawalin wasannin duniya.

Baya ga haka, masu sukar shirin da ƙungiyoyin kare muhalli sun nuna damuwa kan tasirin hakan, suna cewa yawan tafiye-tafiye da shirye-shiryen gasar mai girma haka zai haifar da matsaloli ga muhalli da kuma rage ingancin gasar.

Sai dai ga ƙasashen Kudancin Amurka kamar Argentina, Paraguay da Uruguay, wannan faɗaɗa na iya zama wata babbar dama, domin zai ba su damar karɓar baƙuncin karin wasanni fiye da guda uku da aka riga aka ware musu a matsayin wasannin bude gasar.

A halin yanzu dai, FIFA ta ce wajibi ne a gare ta ta yi nazari kan duk wata shawara da ta fito daga mambobinta, amma har yanzu ba a mayar da batun faɗaɗa gasar zuwa ƙasashe 64 a matsayin babban tsari na gwamnatin ta ba.

By ukarofi