An gudanar da taron addu’o’in neman ƙarin zaman lafiya a Kano

Spread the love

Daga DAUDA USMAN

A ranar Asabar ɗin makon da ta gabata ne wani fitaccen ɗan kasuwar gwari a Legas, Alhaji Ubale Babu Munafinci, ɗan asalin ƙaramar Hukumar Kiru a Jihar Kano, ya jagoranci wani babban taron addu’o’in neman ƙarin zaman lafiya a Kano, Legas da ma ƙasa baki ɗaya.

Alhaji Ubale, wanda ya shahara a harkokin kasuwancin gwari a babbar kasuwar Mile 12 International Market da ke birnin Legas, ya shirya taron ne a harabar gidansa da ke garin Kiru.

Taron ya samu halartar manyan malamai, magada da sarakuna, ciki har da Injiniya Kabiru Kiru, tare da tawagar ’yan kasuwar Mile 12 International Market da kuma ɗumbin al’umma daga sassa daban-daban na ƙaramar Hukumar Kiru da kewayenta. Daga cikin fitattun ’yan kasuwar da suka halarta akwai Alhaji Dauda Tarai, tsohon sakataren ɓangaren kasuwancin tattasai a Mile 12, Alhaji Kabiru Yalo da sauransu.

Haka kuma, uban taron, mai girma mai garin Cunkoso da ke ƙaramar Hukumar Madobi, Alhaji Yusif Isma’il, ya halarci taron.

Tun daga farkon buɗe taron da addu’a, malamai da suka halarta sun gabatar da wa’azuzzuka ga al’ummar Musulmi, inda suka yi bayani kan kusantowar watan azumin Ramadan da kuma muhimmancin ciyar da al’umma a wannan wata mai alfarma.

Malaman sun kuma karanto ayoyin Alƙur’ani mai tsarki tare da gudanar da addu’o’i na musamman, suna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da ya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a Jihohin Kano da Legas da ma Nijeriya gaba ɗaya.

A yayin taron, babban limamin masallacin Juma’a na garin Kadauji, Malam Sha’aibu Kadauji, ya jagoranci sauran malamai wajen ɗaura aure a bainar jama’a. An ɗaura auren ’ya’yan Alhaji Ubale Babu Munafinci, wato Ziladaini da amaryarsa Malama Humaira, da kuma Isma’il da amaryarsa Malama Lauratu, tare da yi musu fatan samun zaman lafiya da albarka a rayuwarsu.

A nasa jawabin, Alhaji Ubale Babu Munafinci Kiru ya bayyana matuƙar godiyarsa ga dukkan mahalarta taron.

Ya musamman gode wa tawagar ’yan kasuwar Mile 12 International Market ƙarƙashin jagorancin shugabansu, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam, da malamai da al’ummar ƙaramar Hukumar Kiru bisa amsa gayyatar da suka yi.

Ya kuma yi fatan kowa zai koma gida lafiya, tare da yaba wa shugabannin kasuwar Mile 12 bisa ƙoƙarinsu na haɗa kan ’yan kasuwa da kuma kawo ci gaba a kasuwar.

Daga ƙarshe, ya jawo hankalin ’yan kasuwar da su ci gaba da bai wa shugabanninsu haɗin kai da goyon baya domin tabbatar da ci gaban kasuwar baki ɗaya.

By ukarofi