Yadda aka gudanar da taron walimar buɗe sabon masallacin Juma’a na Saudat a Kano

Spread the love

Daga DAUDA USMAN

A ranar Juma’ar makon da ya gabata, kwamitin gudanar da harkokin sallar Juma’a tare da ayyukan addinin Musulunci na sabon masallacin Saudat Masjid, wanda Injiniya Alhaji Sani Gwarzo ya gina, da ke unguwar Tudun Filani Na’ibawa a ƙaramar hukumar Kumbotso (da kuma wani ɓangare na Tarauni) a cikin garin Kano, ya shirya gagarumin taron walimar buɗe wannan masallaci domin al’ummar Musulmi su ci gaba da gudanar da sallar Juma’a da sauran ibadu.

Taron ya samu halartar dumbin al’ummar Musulmi daga sassa daban-daban na ƙananan hukumomin jihar Kano, musamman mabiya ɗarikun Tijjaniyya da ƙadiriyya. Mahalarta taron sun haɗa da malamai, magada annabawa, matasa, dattawa, da kuma ’ya’yan marigayi Sheikh Malam Nasiru Kabara da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin addini.

Babban baƙon taron shi ne Alhaji Musa Jidda Dan’adalen Mubi, tare da sauran manyan baƙi. A wajen taron, Khalifan Sheikh Nasiru, Sheikh Nasiru Nasiru, shi ne ya kasance babban limamin masallacin, kuma shi ne ya jagoranci al’umma a sallar Juma’a. A cikin hudubarsa, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ƙara ƙoƙari wajen aikata ayyukan alheri a kowane lokaci, ba sai a watan azumin Ramadan kaɗai ba.

An bayyana cewa Injiniya Alhaji Sani Gwarzo, tsohon Manajan Darakta na Hadeja da Jama’are, shi ne ya assasa gina wannan katafaren masallaci, inda ya sadaukar da shi ga mahaifiyarsa domin ta ci gaba da samun lada da tubarraki. Wannan aiki nasa ya samu yabo daga mahalarta taron.

A nasa jawabin, babban baƙo Alhaji Musa Jidda Dan’adalen Mubi ya fara da godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa ba shi damar halartar wannan muhimmin taro.

Ya kuma yaba wa Injiniya Sani Gwarzo bisa wannan babban aikin alheri da ya aiwatar, yana mai jaddada muhimmancin irin waɗannan ayyuka ga cigaban addini da al’umma. Haka kuma, ya yi kira ga sauran masu hali da su yi koyi da wannan aiki domin neman falala a ranar Lahira.

A ƙarshe, Injiniya Alhaji Sani Gwarzo ya gabatar da nasa jawabin godiya ga dukkan al’ummar Musulmi da suka halarci taron, yana mai nuna farin cikinsa bisa yadda suka amsa gayyata. Ya kuma yi musu fatan alheri tare da addu’ar komawa gida lafiya.

Taron walimar buɗe masallacin ya kasance abin tarihi da ya nuna haɗin kai, kauna da kuma kishin addini a tsakanin al’ummar Musulmi na jihar Kano.

By ukarofi