
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata Babbar Kotu a Lokoja ta umarci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ta biya diyyar Naira biliyan 1 akan wata ƙara da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya shigar.
Kotun ta ce bisa la’akari da hujjojin da kuna ƙoƙarin warware matsaloli, ta yi hukuncin bai wa wanda ya shigar da ƙarar nasara.
Mai Shari’a A. S. Ibrahim yayin hukuncin, ya bayyana cewa yayin kammala ƙarar, batutuwa biyu da aka yi nazari akan su sun nuna cewa wanda ya shigar da ƙarar ya yi nasara.
Da fari dai akwai batun yaɗa kalaman ɓatanci akan wanda ya shigar da ƙarar a wata hira da aka yi a gidan talabijin na Arise, wanda hakan ya zubar da mutunci ne ga tsohon gwamnan.
Haka kuma, wanda ke tuhumar ta bayyana wanda ya shigar da ƙarar a matsayin wanda ya yi kisa, makashi, mai haddasa munanan ayyuka kuma barazana ga mutanen Kogi ba tare da wata hujja ba.
Akan haka ne kotun ta haramta wa wanda ake zargi ko makusantanta da kada su sake yin wasu kalamai da suka shafi cin fuska ga mai ƙarar a gidajen talabijin ko rediyo.
Akan haka ne kotun ta umarci Sanatar da ta biya diyyar biliyan N1 ga Yahaya Bello.
Duk da cewa Natasha ta ɗaukaka ƙara akan al’amarin na haramta wa kotun aiki akan shari’ar a Kotun Ɗaukaka Ƙara, kotun ta yi watsi da buƙatar.
