Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Masana’antu ta Nijeriya (MAN) ta bayyana rashin amincewarta da shawarar Bankin Duniya wadda ke ba da shawarar a sake ba da lasisin shigo da man fetur, tana mai cewa hakan na iya jefa ci gaban masana’antu cikin haɗari.
A wata sanarwa da ta fitar a Legas, Darakta Janar na MAN, Segun Ajayi-Kadir, ya ce ƙungiyar ta nazarci rahoton sabunta tattalin arzikin Nijeriya na watan Afrilu 2026 da Bankin Duniya ya fitar, inda ya jaddada cewa sun ƙi amincewa da hujjar cewa sake buɗe shigo da fetur zai rage hauhawar farashi.
A cewarsa, wannan shawara tana da kura-kurai masu yawa kuma za ta iya lalata irin ci gaban da aka samu wajen ƙarfafa masana’antu a cikin gida. Ya yi gargaɗin cewa ƙara dogaro da shigo da man fetur zai ƙara matsin lamba kan kuɗaɗen musayar waje, ya raunana darajar naira, tare da ƙara tsadar kayan masarufi da injuna da masana’antu ke amfani da su.
Ajayi-Kadir ya bayyana cewa babban abin da ke haddasa hauhawar farashi a Nijeriya shi ne matsalolin da suka shafi canjin kuɗi, yana mai cewa ƙara shigo da fetur ba zai magance matsalar ba, sai dai ma ya tsananta ta.
Har ila yau, ya nuna cewa dogaro da man fetur na waje zai sa darajar tattalin arziki ta rika fita ƙasashen waje, ya raunana ƙoƙarin tace mai a cikin gida, tare da jefa ƙasar cikin haɗarin tangarɗa idan aka samu matsala a kasuwannin duniya.
Shugaban na MAN ya bayyana dakatar da bayar da lasisin shigo da fetur a matsayin wani muhimmin gyaran tsarin tattalin arziki, wanda ke tallafa wa samar da kayayyaki a cikin gida da kuma riƙe kuɗi a cikin ƙasa. Ya kuma yi gargaɗin cewa janye wannan tsari na iya rusa nasarorin da aka samu a fannin tace mai a cikin gida, ciki har da gudunmawar matatar Dangote.
A matsayin mafita, ya buƙaci a ƙara inganta aiwatar da manufofin gwamnati kamar tsarin “naira-for-crude” domin tabbatar da wadataccen mai ga matatun cikin gida. Haka kuma, ya buƙaci a hanzarta aiwatar da shirin amfani da iskar gas (CNG), musamman ta hanyar tallafa wa masu ababen hawa wajen sauya injinansu domin rage tsadar sufuri da jigilar kayayyaki.
Bugu da ƙari, Ajayi-Kadir ya nemi a ba masana’antu tallafi na musamman, ciki har da kawar da cikas a kasuwanci, cire harajin kashi huɗu na FOB, da kuma samar da rance mai sauƙin ruwa. Ya kuma jaddada muhimmancin zuba jari a bangaren wutar lantarki domin rage dogaro da man fetur mai tsada wajen gudanar da harkokin masana’antu.
A ƙarshe, ya nanata cewa dorewar ci gaban tattalin arzikin Nijeriya na rataye ne a kan ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida maimakon ƙara dogaro da shigo da kaya daga ƙasashen waje.
.
