An naɗa ɗa ga Dikko Raɗɗa sarautar Gwagwaren Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya naɗa Alhaji Muhammadu Dikko Raɗɗa a matsayin sabon Gwagwaren Katsina na II kuma Hakimin Raɗɗa, a wani gagarumin biki da ya gudana a fadan Sarkin Katsina.

Haka kuma an naɗa Alh. Abubakar Dardisu a matsayin Sarkin Mudurun Katsina Hakimin Muduru, sai Ahmed Abdulmumini Kabir Usman ɗa ga mai martaba Sarkin a matsayin Ɗan Majen Katsina Hakimin Dankama.

Sabon Gwagwaren Katsina na II da aka naɗa, ɗa ne ga Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya zama hakimin farko na sabuwar masarautar Raɗɗa da aka ƙirƙira a ƙaramar hukumar Charanchi.

Da yake gabatar da jawabi bayan kammala naɗe-naɗen Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya bayyana sabbin hakiman a matsayin mutane masu tarihi na sarauta kuma halayen su na ƙwarai na daga cikin abubuwan da aka kula da su kafin basu sarautun.

Bikin ya samu halartar manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya, ciki har da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, Mataimakin Gwamnan Katsina Faruk Lawal Jobe, Mataimakin Gwamnan Jigawa Injiniya Aminu Usman Gumel, Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin siyasa Ibrahim Kabir Masari, Gwamnan Zinder Massalatchi Mahamam Sani, Sarkin Daura Faruk Umar Faruk, da Sarkin Damagaram (Zinder) Aboubacar Oumarou Sanda, tare da sauran manyan baƙi masu daraja.

By ukarofi