Dambe wasar maza, kowwayyi hankali ya barka: Waiwaye kan tarihin kiɗan dambe na Dan’anace (3)

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD 

(Danmadamin Birnin Magaji)

Waƙoƙin jama’a:

Waƙar Sani Kangiwa 1937-2010 (73)

Sunan wanda aka yi ma waƙa Alhaji Sani Adamu ɗanbaba Kangiwa Turakin Kebbi / Argungu

Shekarar da aka yi waƙa 1978

Muhallin Waƙa  ƙofar Tsohon Gidan Alhaji Sani Kangiwa da ke Sakkwato

Saƙon Mawaƙi/Waƙa Yabo da Kambamawa

Waƙar Zubairu ƙofar Rini 1940-1993 (53)

Sunan wanda aka yi ma waƙa Alhaji Zubairu Tela ɗanmalikin Sakkwato

Shekarar da aka yi waƙa 1976

Muhallin Waƙa  ƙofar Gidan Alhaji Zubairu Tela ƙofar Rini Sakkwato

Saƙon Mawaƙi/Waƙa ƙauna da Soyayya 

Waƙar Aliyu Layi 1934-2002 (68)

Sunan wanda aka yi ma waƙa Alhaji Aliyu Layi Sakkwato

Shekarar da aka yi waƙa 1977

Muhallin Waƙa  ƙofar Gidan Alhaji Aliyu Layi da ke Sakkwato

Saƙon Mawaƙi/Waƙa Yabo da Kambamawa 

Waƙar Alhaji Mamman Na-Gwambe 1912/01/1936 – 17 /09/1986 (50)

Sunan wanda aka yi ma waƙa Alhaji Dr. Muhammad Inuwa Gwambe

Shekarar da aka yi waƙa 1979

Muhallin Waƙa  ƙofar Gidan Alhaji Mamman Gwambe Lamba 1, Layin Jaɓɓi (Jabi), Garin Kaduna, Kaduna.

Saƙon Mawaƙi/Waƙa Yabo 

Waƙar Alhaji Shehu Sakkwato 1935-2015 (80)

Sunan wanda aka yi ma waƙa Alhaji Usaman Kure (ɗangaladiman Bunguɗu/ Usman Na-Makurɗi)

Shekarar da aka yi waƙa 1975

Muhallin Waƙa  ƙofar Gidan Alhaji Usman Kure, Reliwe Kwatas Kano

Saƙon Mawaƙi/Waƙa Yabo 

Waƙar Alhaji Bappa Gwaram 1942-2000 (58)

Sunan wanda aka yi ma waƙa Alhaji Muhammadu Bappa Gwaram, Jigawa

Shekarar da aka yi waƙa 1975

Muhallin Waƙa  ƙofar Gidan Alhaji Usman Bappa Gwaram a Jigawa

Saƙon Mawaƙi/Waƙa Yabo  

Waƙoƙin sarakuna: 

Waƙar Sarkin Sudan Shehu Malami 1937-2022 (85)

Sunan wanda aka yi ma waƙa Alhaji Shehu Malami OFR, CON

Shekarar da aka yi waƙa 1975

Muhallin Waƙa  Fadar Maigirma Sarkin Sudan da ke Wurno, a Garin Wurno Sakkwato

Saƙon Mawaƙi/Waƙa Tarihi (Taskace Asali da Nasaba)

Waƙar Sarkin Kudu Mahammdu Macciɗo 1928-2006 (78)

Sunan wanda aka yi ma waƙa Alhaji Bello Muh’d Macciɗo, CON

Shekarar da aka yi waƙa 1979

Muhallin Waƙa  Gidan Sarkin Kudun Sakkwato, Kanwuri, Sakkwato

Saƙon Mawaƙi/Waƙa Tarihi (Kirari) 

Waƙoƙin dambe:

Waƙar ɗan ɗambe Ango Dangiye 1918-2008

Sunan wanda aka yi ma waƙa Muhammadu Ummaru (Ango ɗangiye) ‘Yartsakkuwa

Shekarar da aka yi waƙa 1937

Muhallin Waƙa  Tsakkiyar Kassuwar Garin Tumba, Bakura, Zamfara

Saƙon Mawaƙi/Waƙa Tarihi Zuga 

Waƙar ɗan dambe Ummaru Gundumi 1942-Zuwa Yau

Sunan wanda aka yi ma waƙa Ummaru Gundumi Boma, Koko Besse, Kebbi

Shekarar da aka yi waƙa 1969

Muhallin Waƙa  Damagaram, Jamhuriyar Nijar

Saƙon Mawaƙi/Waƙa  Zuga

Waƙar ɗan dambe Bagobir 1940-Zuwa Yau Dawo-Dawo Bagobiri….

Sunan wanda aka yi ma waƙa Alhaji Yahya Ibrahim Bagobiri (ɗan-Tcimau) Bargaja, Isah, Sakkwato

Shekarar da aka yi waƙa 1964

Muhallin Waƙa  Garin Kano, Jihar Kano

Saƙon Mawaƙi/Waƙa  Zuga 

Waƙar ɗan Dambe Dogo Miko 1936 -1974*

Sunan wanda aka yi ma waƙa Mika’ilu Ban-Dawa ‘Yan-kwashi, Jigawa

Shekarar da aka yi waƙa 1969

Muhallin Waƙa  Garin Kano, Jihar Kano

Saƙon Mawaƙi/Waƙa  Zuga  

Waƙar Dan Dambe Ado ɗankore 19??

Sunan wanda aka yi ma waƙa Adamu ɗankore Kano

Shekarar da aka yi waƙa 1969

Muhallin Waƙa  Garin Kano, Jihar Kano

Saƙon Mawaƙi/Waƙa  Zuga 

Waƙar Dan dambe ɗandunawa ɗansarki, Ka-wurin Kuɗi, Zango ,

Daura, Katsina,19??

Sunan wanda aka yi ma waƙa ɗandunawa, 

Shekarar da aka yi waƙa 1955

Muhallin Waƙa  Garin Kano, Jihar Kano

Saƙon Mawaƙi/Waƙa  Zuga

Zumuntar Hanta da Jini : Dan’anace da Shago

A shafin rataye na tattaunawa da ɗan’anace, ya bayyana cewar koda ya haɗu da Shago yana waƙoƙin dambe da na noma da na jama’a. Hasali ma ba Shago ya fara yi ma waƙoƙin dambe ba. Shagon kansa ya gaya ma ɗan’anace a kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Kuryawajen wasa, cewar “har da waɗanda ba kowa ba a harkar dambe, ka yi musu waƙa, sai ni kaɗai ya rage in samu albarkar bakinka.” A shaidawar ɗan’anace zuwa ga Shago, ko lokuttan da ka nemi a yi maka waƙa gabanin wannan karon ba a yi ba, “waƙar ce ba ta zo ba” Daga rannan dai Shago ya shiga bakin ɗan’anace, waƙa ta samu.

Gusau, (1997:216-224) ya bayyana a tsakurensa kan makaɗa ɗan’anace cewar, da Shago da ɗan’anace kowa ya hidda sunan wani. Wato sun samu ɗaukaka a zamaninsu sanadin haɗuwa da juna. A shaidawar Gusau, (1996), ɗan’anace ya bayyana cewa, duk sadda aka ganni a wani wuri ko wani gari, ko a gidan wani, ko a fagen wajen wasa, to sai an tambaye ni Shago. Shi ma Shago duk inda ya taka ƙafarsa, sai an tambaye shi ina Dan’anace?. “Kai ko bayan wafatimmu in mun bar duniyagga, duk wanda yay yi maganar ɗan’anace, sai an ambato Shago” 

ɗan’anace ya sake shaidarda cewa a cikin tattaunawar da aka kawo shafunan Rataye cewar bayan Shago ya yi ritaya daga sana’ar dambe, daga shekarun 1972, zumunta shi da ɗan’anace bata yanke ba, domin suna kai wa juna ziyara. Kuma idan ɗan’anace ya je gidan Shago, yana shiga har turakarsa, da kuma ruhewarsa, ya yi walkami da kayan duk da ya gani yana so a cikin gidan Shago, kuma ya ɗauki duk abinda yake so, zuwa gidansa. Soyayya tsakanin Shago da ɗan’anace ta ci gaba da wanzuwa har da mutuwa ta raba su.

Yahaya ɗan’anace ya shaidarda, zuri’ar waɗannan mutane biyu wato Shago da ɗan’anace sun mayar da wannan ƙauna ta iyayensu zumunci, inda Yahaya, ya auri ɗiyar Shago mai suna Faɗimatu. Iyalan Shago da na ɗan’anace sun mayar da zuri’arsu tamkar ɗaya domin a koda yaushe suna zumuncin bukukuwa da na alhini da kuma ziyarar sada zumunci a kai a kai.

Bakandamiyar ɗan’anace Waƙar Shago 

Duk mawaƙin da yas shahara yana da bakandamiyar a cikin waƙoƙinsa. Bakandamiyar waƙa tana nufin waƙar da mawaƙi ya fi so ko kuma masu saurare suke so daga cikin waƙoƙinsa. Waƙar ƙumshiyarta cike take da zalaƙar harshe wadda aka gina tsawon lokaci ana rerawa ana yi mata ƙari. Daga cikin waƙoƙin ɗan’anace, Waƙar da ya yi ma Shago ita ce ya ayyana a matsayin bakadamiyarsa. Ga buɗewar waƙa:

J. Tooh  Bahago, 

‘Y Ina mazan da ka ii maah?

J. Karo da Duna ba shi da daɗi

‘Y. Baleri ba guda da guda ba,

J. Ina gidammu zaune da sahe

Dan Audu yai iske ni,

Yac ce mu zo ni Gandi Dambe,

Mun zo ni Gandi Dambe,

Ana kirammu Rara da Hwama,

Yacce ɗan’anace mai buga kawu,

Shirya mu je ni Rara Dambe,

Kuma na ce Dan’anace ba ni da dama

Wandara kasan abinga ba ya da daɗi,

‘Y. Kak ka kashe mutum, ka bar ni a kamman,

 J. Kada ka kashe mutum, ka banni a kamman

 ‘Y Ka banni a kamman garinga ba ni da kowa

Wannan waƙa ta naɗe tarihi, domin bayan ayyanata a matsayin bakandamiya, kuma itace aka rera wa Shago a lokacin da suka  shirya amsa katin gayyatar mutanen Kuryar Gandi a shekarar 1943. ɗan’anace ya rerawa wa Shago wannan waƙa domin fuskantar aboakanin wasansa na dambe a garin Kurya. Waƙar tana cike da salon Zuga da washi domin kowane layin waƙa rana amfani da kalmar da ke tsima ɗan Dambe a filin wasa. Kalmomi kamar Baleri, da Duna, Gazaguru, ba Guda da guda ba, duka kalmomi ne da ke nuna jarumtaka. 

Naɗewa:

A cikin naɗewar wannan tsakure, zan so in bayyana tasirin da waƙoƙin Muhammadu Bawa ɗan’anace suka yi mini a rayuwata ta yau da kullum. Allah bai sa na yi ido biyu da makaɗa Bawa ɗan’anace ba, domin koda nit tahi kai ziyarar aiki ta neman tarihin, makaɗa Bawa ɗan’anace a ‘Yartsakkuwa a shekarar 1989, na tarar ya shekara ukku (3) da wafati. Waɗanda nit taras, iyalansa ne, da masu taya shi aikin waƙa. Bayan na yi musu ta’aziyya, na tambaye su, kan rayuwa da fasaharsa. A nan ne bincikena a kansa ya fara har zuwa kawowa yau, da nike gabatar da ɗan abinda nis samu tsawon shekaru talatin da bakwai (37).

An ga rukunnan waƙoƙin ɗan’anace bisa fahimtar ƙumshiyarsu, a shafi na 14 zuwa 17 lamba ta 4.2. an kawo samfurin waƙoƙin gargajiya waɗanda ɗan’anace ya fara yi na bukukuwan al’ada a ƙauyukansu. Waɗannan waƙoƙi sun tunatar da ni tsofaffin al’adun Hausawa musamman na mazauna ƙauyuka. Waɗannan al’adu su ne suke riƙe da sunan Hausawa zuwa yau, misali waƙoƙin aure da na bukukuwan Sallah 

Rukunin waƙoƙin ɗan’anace na Sarakuna sun ƙara nuna cewa, makaɗi in ya je wajen Basarake ko attajiri ko yana da kuɗɗi, to yana duƙar da kansa bisa girmamawa ga wanda yake yi ma waƙa. Waƙar Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu Macciɗo, da waƙar Sarkin Sudan na Wurno, ƙumshiyarsu ta bayyana yadda bara (makaɗi) kan girmama ubangidansa Basarake.

Waƙoƙin jama’a irin su Alhaji Sani Kangiwa, Turakin Kebbi, da Alhaji Aliyu Layi Sakkwato sun bayyana yadda makaɗi ke adana tarihin manayan mutane. ɗan’anace ya kwanta dama, Aliyu layi da Sani Kangiwa duka sun kwanta dama, amma waƙoƙin ɗan’anace sun sa yau mun tuna da su, kuma ana kan tunawa da su har koyaushe aka waiwayo waƙoƙinsu da ɗan’anace ya yi musu. Rukunin waƙoƙin ‘Yan Dambe sun ilmatar da mu cewa akwai wasu wasanni na Hausawa da dole sai da kiɗa na zuga suke iya kasancewa in babu kiɗa, Dambe da kokawa da tauri da farauta duk kiɗi shi ke tsima ‘yan wasa har su yi abinda ba a yi tsammani ba. Na samu ilmi ƙwarai kan yadda ‘yan dambe kan kimtsa jikinsu ta hanyar neman magunguna na sha da na wanka wasu lokutta har da tsafi domin samun waibuwa da nasara a fagen wasa. Dambe na ɗaya daga cikin al’adun gargajiya da ya kafa tarihin jarumai da jarumtaka tsawon lokaci.

Waƙar Twanka ƙanen Sule ta nusar da ni kan kada in yarda gardama ta haɗa ni da wani, har sanadiyyar hakan, a kai ni gaban ƙuliya, ko kuma ni in kai wani gaban alƙali, wannan waƙa ta koya mini haƙuri a fawalla ma Allah dukkanin lamarina. 

Waƙar Garba Na-godi akwai ɗan waƙa kan mutuwa da ya tsinke kuzarina. ‘Ashe mutum ba komi na ba, ranar mutuwa rai ya alace. Ka so mutum rannan ka rasa shi, kai ta kira bai amsa kira ba, ka koma kira bai karɓa kira ba, sai mutuwa ɗai adda hakanga’ kuma a cikin waƙar Miko Dogo ɗan’anace na cewa ‘ita duniyagga duk yadda taɗ ɗau mutum tanai masa jakkab bawa’ bayan ta ɗaga mutum sama ta hanyar ɗaukaka shi, sai ta kashe shi ƙasa kuma ranar mutuwa sai rayuwarsa ta  wahala kafin ransa ya fita kamar ba shi ne ya buga taƙama ba, a zamaninsa. A cikin waƙar Bagobiri ɗan’anace, ya ce ‘Wata rana waɗansu ne, mu mun wuce, zamani duniyagga lamarinki tsoro nai nikai’

Allah ya sa mu gama da duniyagga lafiya, amin.

By ukarofi