An ɗaure matashi rai-da-rai kan yi wa yarinya fyaɗe

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wata kotun sauraron ƙararrakin iyali da ke Kalaba a Jihar Kuros Ribas, ta yanke wa wani matashi mai suna Nyojole hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan samunsa da laifin yi wa wata yarinya mai shekara 13 fyaɗe. 

Mai shari’a Blessing Egwu ta ce kotun ta gamsu da hujjoji da shaidu da aka gabatar, ciki har da takardun gwajin asibiti da suka tabbatar da aikata laifin.

Shaidu sun bayyana cewa wanda aka yankewa hukuncin ya yaudari yarinyar zuwa wani kango a yankin ƙaramar Hukumar Kalaba ta Kudu, inda ya ba ta Naira 1,600 kafin aikata laifin.

Kazalika, bayanai sun ce wani abokinsa da ake zargi da hannu a lamarin ya tsere bayan faruwar lamarin.

Lauyan Hukumar Kare Haƙƙin ɗan Adam ta BRCI, James Ibor, ya yaba wa hukuncin kotun, yana mai cewa hakan zai zama izina ga masu aikata irin wannan laifi.

By ukarofi