Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani mai goyon bayan Injiniya Muazu Jaji Sambo a Jihar Taraba, Naseeru Taneemu Annuree, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC na ƙasa da na jihar Taraba da su bai wa tsohon Ministan Sufuri, Mu’azu Jaji Sambo, tikitin takarar gwamnan jihar Taraba domin ceto jihar da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa ga al’umma.
Naseeru Taneemu Annuree ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai kan halin da siyasar jihar Taraba ke ciki da kuma shirye-shiryen jam’iyyar APC gabanin zaɓe mai zuwa.
Ya ce babu shakka Mu’azu Jaji Sambo na daga cikin mutanen da suka fi cancanta su jagoranci jihar Taraba duba da irin ƙwarewa, gogewa, ilimi da kuma kyakkyawan tarihin hidimar jama’a da ya nuna a lokacin da yake Ministan Sufuri na Tarayyar Nijeriya.
A cewarsa, lokacin da Mu’azu Jaji Sambo yake Minista, ya nuna kishin ƙasa da jajircewa wajen bunƙasa harkokin sufuri da kuma inganta hanyoyin kasuwanci da sufuri da suka taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa tsohon ministan ya kasance mutum mai tawali’u da kusanci da talakawa, wanda ko bayan saukarsa daga muƙami bai manta da al’ummar jihar Taraba ba, domin ya ci gaba da gudanar da ayyukan more rayuwa da samar wa matasa aikin a matakai daban-daban.
“Mu’azu Jaji Sambo mutum ne mai hangen nesa da tsoron Allah. Mutum ne da ya san yadda ake tafiyar da mulki cikin gaskiya da riƙon amana. A lokacin da yake Ministan Sufuri, ya nuna ƙwarewa da nagarta sosai, har ma da waɗanda ba ‘yan jam’iyyarsa ba suna yabonsa,” inji Annuree.
Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin abubuwan da suka ƙara fito da cancantar Mu’azu Jaji Sambo shi ne yadda yake taimakawa matasa da mata ta hanyar samar musu da tallafi da ƙarfafa su wajen dogaro da kai.
A cewarsa, dubban matasa a Taraba sun amfana da shirye-shiryen horaswa da tallafin kasuwanci da ya samar, yayin da da dama daga cikinsu suka samu aikin yi ko suka fara sana’o’insu domin rage zaman banza da talauci.
Naseeru Taneemu Annuree ya kuma ce Mu’azu Jaji Sambo ya taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan al’ummar Taraba ba tare da nuna bambancin ƙabila, addini ko yanki ba, yana mai cewa wannan halayya tasa ce ta sa mutane da dama ke ganin shi ne mafita ga jihar.
Ya ce jihar Taraba na buƙatar shugaba mai hangen nesa, wanda zai iya jawo manyan ayyukan raya ƙasa, zuba jari da kuma bunƙasa tattalin arziki kamar yadda Mu’azu Jaji Sambo ya nuna a rayuwarsa ta siyasa da ta aiki.
Annuree ya bayyana cewa idan APC ta bai wa Mu’azu Jaji Sambo tikitin takara, jam’iyyar za ta samu karɓuwa sosai a tsakanin al’umma tare da ƙaruwa mai yawa na magoya baya daga sassa daban-daban na jihar.
“Al’ummar Taraba suna buƙatar shugaba mai gaskiya da riƙon amana. Mu’azu Jaji Sambo ya nuna cewa shi mutum ne mai son ci gaban jama’a. Yana taimakon marasa galihu, yana tallafa wa matasa, yana ƙarfafa mata, kuma yana kula da harkokin ilimi da lafiya,” inji shi.
Ya ƙara da cewa tsohon ministan ya kasance mai sauraron jama’a kuma shugaba ne wanda yake karɓar shawarwari daga kowa ba tare da nuna girman kai ba.
Naseeru Taneemu Annuree ya yi kira ga ‘ya’yan APC a Taraba da su haɗa kai tare da marawa Mu’azu Jaji Sambo baya domin bai wa jam’iyyar damar samun nasara a zaɓe mai zuwa.
Ya ce lokaci ya yi da al’ummar Taraba za su zaɓi shugaba mai inganci wanda zai kawo ci gaba a fannoni kamar ilimi, lafiya, noma, tsaro, hanyoyi da samar da ayyukan yi ga matasa.
A ƙarshe, ya bayyana cewa Mu’azu Jaji Sambo mutum ne mai cikakken ƙwarewar shugabanci wanda zai iya sauya fasalin jihar Taraba tare da ɗaga martabarta a matakin ƙasa baki ɗaya idan aka ba shi damar jagoranci.
