Baba-Ahmed ya yi kakkausar suka ga Obi kan ficewa daga Jam’iyyar LP

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Datti Baba-Ahmed, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar LP, ya soki Peter Obi kan ficewa daga jam’iyyar a lokacin da ake fama da rikicin cikin gida a maimakon tsayawa ya yi ƙoƙarin warware matsalar.

Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a ranar Litinin jim kaɗan bayan sauya sheƙa daga LP zuwa PRP a Abuja. An ɗauki kalaman nasa ne a wani bidiyo da yake yawo a shafin Facebook.

Sukar tasa na zuwa ne bayan da Obi da Kwankwaso suka sauya sheƙa daga ADC zuwa wanda ya jawo hasashen cewa akwai yuwuwar su yi takara tare a shekarar 2027.

Obi ya yi takarar shugaban ƙasa a 2023 a jam’iyyar LP, sai dai ya bar jam’iyyar saboda rikicin shugabanci. Daga baya ya faɗa jam’iyyar ADC. Sai dai daga baya an samu ɓullar rikicin shugabanci.

A yayin da yake magana kan al’amuran siyasa, Baba-Ahmed ya ce ficewar Obi daga jam’iyyar LP bai dace ba. Ya ce bayan cin moriyar jam’iyyar, akwai nauyi a kan Obi na tsayawa domin magance matsalolin da suka taso.

“Mutumin da ya samu takara a Labour Party (takarar shugaban ƙasa a 2023) cikin sauƙi, ya kamata ya tsaya a gyara matsalolin da suka taso da shi, kuma komai wahalarsu,” ya bayyana.

Ya ƙara da cewa ya tsaya kan samar da masalaha a jam’iyyar, sai dai bai ji daɗin matakin da Obi ya ɗauka ba.

“Na tsaya na fuskanci fushin wasu saboda na ce ‘ku zo a yi sulhu’ a LP,” ya faɗa.

“Sai kawai ji na yi tsohon jagoran jam’iyyar yana cewa ba zai zauna a duk inda ake husuma ba. Don haka idan akwai rashin jituwa a Najeriya, shin fita za ku yi ku bar ƙasar? Akwai abin da ba daidai yake ba.”

A game da haɗakar Obi da Kwankwaso, Baba-Ahmed ya nuna shakkunsa kan tasirinsu musamman a Arewacin Najeriya.

“Yanzu suna tare da Kwankwaso, wannan tunanina ne. Zai yi aiki? Ina ga wannan babbar tambaya ce. Za mu jira mu gani,” ya faɗa.

Sanann ya ƙara da cewa, ya ce takarar cike take da abubuwan tambaya, musamman game da tsarin daidaito.

A yayin da yake magana game da shekaru da gogewa da mtsayi na siysa.

“Mataimakin shugaban ƙasa ya girme shi a shekaru. A ɓangaren siyasa, waye kenan zai zama shugaban ƙasa,?” ya faɗa.

Baba-Ahmed ya ƙarƙare da cewa duk wani rabo na tikitin tsayawa takara da ake so ya yi nasara cike yake bin wasu matakai.

By ukarofi