Abdul Samad Rabi’u ya kere Johann Rupert a matsayin mutum na biyu da ya fi arziƙi a Afirka

Spread the love

Sanannen attajirin ɗan kasuwa a Nijeriya, Abdul Samad Rabiu, ya zama mutum na biyu mafi arziƙi a Afirka bayan dukiyarsa ta haura dala biliyan 18.6, kamar yadda jerin masu kuɗi na Bloomberg Billionaires Index ya nuna.

Rahoton ya ce Rabiu ya zarce attajirin Afirka ta Kudu, Johann Rupert, wanda dukiyarsa ta ragu zuwa dala biliyan 17.9 a shekarar 2026.

Bloomberg ta bayyana cewa Rabiu ya samu ƙarin arziki mafi yawa a Afirka bana, sakamakon bunƙasar kamfanoninsa na siminti, abinci da masana’antu.

Sabon matsayinsa ya sanya shi a bayan Aliko Dangote kaɗai, wanda har yanzu yake matsayin mutum mafi arziki a Afirka da dukiyar dala biliyan 34.4.

Rahoton ya kuma nuna cewa attajirai ‘yan Najeriya irin su Mike Adenuga da Femi Otedola ba su cikin jerin mutane 500 mafi arziki a duniya na Bloomberg.

By Babaji