Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar APC ta sanya ranar Asabar, 9 Ga Mayu, 2026, don tantance Barista Kashim Musa Tumsah a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen takararsa na gwamna a Jihar Yobe.
Abubakar Ahmed, jakakin ƙungiyar yaƙin neman zaɓen sa yayi wannan jawabi cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Gusau yau Juma’a.
A cewarsa, kwamitin da shugabannin APC suka kafa zai gudanar da tantancewar kuma an shirya gudanar da ita da ƙarfe 1:00 na rana a Transcorp Hilton, Abuja.
Ahmed ya jaddada cewa ana ganin taron a matsayin wani muhimmin mataki biyo bayan bayyanar Tumsah a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen gwamnan Yobe.
“An gayyaci dukkan ‘yan APC, magoya baya, masu biyayya, abokai da ‘yan uwan Tumsah su halarta”.
“Muna sanar da cewa an shirya wani taron kafin taron a Lamba ta 101 Fabian Nworah Avenue, Efab Metropolis Estate, Gundumar Karsana, Abuja, don daidaita zirga-zirgar zuwa wurin taron”.
Ƙungiyar kamfen ɗin ta ce tantancewar ta haifar da sha’awa sosai, inda mutane da yawa ‘yan asalin Yobe da masu fatan alheri suka riga suka yi gangami don bikin.
“Ƙungiyar masu shirya gangamin tana cike da farin ciki da kasancewar ‘yan jihar Yobe da sauran jama’a da ke shirin halartar wannan gagarumin taron,” in ji Abubakar Ahmed.
Tumsah, wanda mutum ne jajirtacce mai kishin ƙasa, ya sanya kansa a matsayin ɗan takarar APC don maye gurbin gwamnan jihar Yobe mai ci.
Ahmed ya ambaci cewa tantancewar ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara samun ƙaruwar ayyukan siyasa a cikin APC yayin da jam’iyyar ke shirin yin zaɓen fidda gwani da kuma babban zaɓen 2027.
