Shettima ya ƙaddamar da shirin raya ƙasa na Majalisar Ɗinkin Duniya a Jami’ar Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafia

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ƙaddamar da shirin Mine-Tech University Innovation Pod (UniPod) na hukumar raya majalisar ɗinkin duniya (UNDP) tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke birnin Keffi (NSUK).

Shettima tare da rakiyar gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule da sauran manyan ‘yan Nijeriya ya ƙaddamar da shirin a jami’ar a ranar Juma’a.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Mine-Tech UniPod da ke NSUK wuri ne da aka kafa domin matasa injiniyoyi masana ilimin ƙasa da ‘yan kasuwa suyi aiki tare da masu bincike da abokan huldar masana’antu domin samar da hanyoyin magance matsalolin sashen ma’adinai na Nijeriya baki ɗaya.

Daga fasahohin haƙowa masu aminci da inganci zuwa ƙirƙire-ƙirƙire da sarrafa ma’adinai da bunƙasa kamfanoni masu tasowa an kuma tsara UniPod din ne domin kama darajar da ke kowane mataki na sarkar ma’adinai.

Shettima wanda ministan Ilimi Mista Tunji Alausa ya wakilce shi ya bayyana Mine-Tech UniPod a matsayin shiri mai tarihi da ke haɗa ilimi da ƙirƙire-ƙirƙire da fasaha da masana’antu da cigaban ƙasa.

“A yau ba kawai ƙaddamar da wata cibiyar jami’a muke yi ba. Muna bayyana hangen nesa na ƙasa baki ɗaya da hangen nesan da ke ganin jami’o’in Nijeriya a matsayin injinan ƙirƙire-ƙirƙire da kasuwanci da bunƙasa ‘yan kasuwa da sauya tattalin arziki,” in ji shi.

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya kuma yaba wa masu ruwa da tsaki da abokan hulɗa bisa hangen nesa da jajircewar da suka nuna wajen farfaɗo da shirin. Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu saboda tabbatar da cewa tsarin Renewed Hope ya sanya cigaban mutane da ƙirƙire-ƙirƙire da masana’antu da ƙarfafa matasa a tsakiyar sauya Nijeriya.

“Yanzu an ɗauki ilimi a matsayin zuba jari na ƙasa da ke da muhimmanci ga cigaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi da cigaban fasaha da fafatawa a duniya,” in ji shi.

Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce duk da Nijeriya tana da ɗimbin albarkatun ƙasa da ake kiyasin sun kai sama da tiriliyan dala gudunmawar sashen ma’adinai ga cigaban cikin gida (GDP) har yanzu tana ƙasa da abin da ya dace.

“Tsawon shekaru muna fitar da albarkatu danye muna shigo da kayayyakin da aka gama a farashi mafi tsada. Muna fitar da damar aiki da fasaha da wadata. Amma yau Nijeriya tana sauya hanya daga haƙowa kawai zuwa ƙara daraja daga fitar da danye zuwa sarrafa masana’antu daga dogaro zuwa cigaban da kirkire-kirkire ke tafiyar da shi.”

“Mine-Tech UniPod ya zo ne a daidai lokacin da ake buƙata a tafiyar mu ta ƙasa. Tattalin arzikin duniya yana shiga sabon zamani da ma’adanai masu muhimmanci ke tafiyar da shi, domin samar da motocin lantarki, tsarin makamashi mai sabuntawa, masana’antu na zamani, batura, na’urorin semiconductor, da fasahohin masana’antu.”

“Mine-Tech UniPod ya dace sosai da waɗannan manufofi. Ra’ayin UniPod da kansa yana canza tsari. Ba cibiyoyin kirkire-kirkire na yau da kullun ba ne, a’a, an sake tunanin tsarin jami’a gaba ɗaya.”

A nasa jawabin gwamna Abdullahi Sule ya yaba da shirin kuma ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar tallafa masa tare da alƙawarin samar da tsarin solar mini-grid domin ɗorewar sa.

Gwamnan ya cigaba da bayyana cewar “Saboda idan ba mu samar da wutar lantarki ba UniPod din zai zama maras amfani. Dole ne a samu wutar da za ta dore. Ba za su iya dogara da janareta ba. Saboda haka za mu samar da solar mini-grid da za ta kasance a can.”

“Za mu kuma cigaba da ƙarfafa abokan huldarmu anan gida Najeriya da ƙasa baki ɗaya don ba dole su gina nasu ba. Amma za su iya yin amfani da wannan damar don bunƙasa fannin. Kuma idan sun yi amfani da shi suna kuma tallafa masa. Haka ne za a iya kula da shi,” in ji gwamnan.

Sauran manyan baƙi da suka yi jawabi a wajen taron ƙaddamar da shirin na musamman na Mine-Tech Unipod a jami’ar da suka haɗa da shugabar jami’ar ta jihar farfesa Sa’adatu Hassan Liman waɗanda ke jagorancin shirin na Mine-Tech Unipod da wakilai daga fannin ma’adanai daga tarayya da jihar ta Nasarawa da sauransu duk sun yaba wa shirin kana suka jaddada mahimmancinsa ga cigaban duka mahimmann ɓangarorin tattalin arzikin ƙasar nan musamman fannin haɓaka ma’adanai da sauransu tare da yin alƙawarin bai wa shirin cikakken goyon baya don cimma burin sa a ƙarshe.

By ukarofi