Hatsarin mota ya yi ajalin mutane 16 a Jihar Kogi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimanin mutane 16 ne suka rasu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a babban titin Lokoja zuwa Okene da ke jihar Kogi.

Rahotanni sun bayyana cewa wata motar haya kirar Toyota Hiace, wadda ke ɗauke da fasinjoji 22 daga jihar Plateau zuwa Lagos, ta gamu da hatsarin ne bayan da direban ya rasa iko da motar, sakamakon gudun wuce ƙa’ida da kuma gajiya.

Motar ta faɗa ƙarƙashin wata gada, lamarin da ya janyo asarar rayuka masu yawa a wurin.

Jami’in Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) a jihar Kogi, Lawal Fagge, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an samu nasarar ceto mutane shida da suka jikkata, kuma an garzaya da su zuwa asibiti domin samun kulawa.

Hukumar ta kuma sake jan hankalin direbobi da su guji tukin ganganci tare da tabbatar da samun hutu kafin fara doguwar tafiya domin kauce wa irin wannan iftila’in.

By Babaji