Rikicin Masarautar Kano: Ni ban ce na amince da Sarki Sanusi ba, inji Ganduje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya musanta amincewa da Muhammadu Sanusi na II a matsayin Sarkin Kano, yana mai cewa Kotun Ƙoli ce kaɗai ke da ikon yanke hukunci akan rikicin masarautar.

Ganduje ya ce duk hukuncin da kotun koli ta yanke, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai mutunta shi tare da aiwatar da shi bisa doka da oda.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa ya amince da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Kano.

Sai dai Ganduje ya ce rahotannin ba gaskiya ba ne, yana mai jaddada cewa kotu ce za ta yanke hukunci na karshe kan rikicin sarautar.

By Babaji