Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 20 a wani sabon hari da suka kai ƙauyen ɗan Gulbi da ke ƙaramar Hukumar Tureta a Jihar Sakkwato.
Wannan ibtila’in na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan wani hari makamancinsa da ya yi sanadin mutuwar mutum 17.
Mazauna yankin sun ce maharan sun mamaye ƙauyen da safiyar Talata da misalin ƙarfe 8:00, inda suka riƙa harbe-harbe kan mai uwa da wabi, lamarin da ya tilasta wa jama’a tserewa domin neman mafaka.
Wata majiya daga yankin ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun shafe sa’o’i suna cin karensu babu babbaka a cikin ƙauyen, inda suka kashe mutane sannan suka ƙona gidaje masu yawa.
“Sun zo ne suka fara harbe-harbe. Mutane suka riƙa gudu ta ko’ina domin ceton rayukansu,” inji majiyar da ta buƙaci a sakaya sunanta.
Majiyar ta ƙara da cewa an yi mummunar ɓarna domin baya ga asarar rayuka, gidaje da dama sun ƙone a yayin harin.
A ranar Lahadin da ta gabata ma, wasu ’yan bindiga sama da 150 ɗauke da makamai a kan babura sun kai hari ƙauyen, inda suka kashe mutum 17 ciki har da wasu mutum bakwai da ke yawon Sallah, tare da wawashe kayayyaki daga kusan shaguna 20.
Da Manhaja ta tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Ahmad Rufai, ya ce tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun tura jami’ai zuwa yankin domin bincike da ɗaukar matakan da suka dace.
Ya ƙara da cewa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar na jiran cikakken bayani daga jami’an da aka aike wurin harin.
