Boko Haram na shirin yin ‘bikin kammala karatun Alƙur’ani’ ga mata da yara sama da 100 da suka sace a Kwara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Iyalan wasu mutanen da aka sace daga ƙauyen Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara sun bayyana cewa wasu ‘yan ta’adda da ake zargin Boko Haram ne na shirin gudanar da bikin kammala karatun Alƙur’ani ga mata da yara sama da 100 da ke hannunsu.

Iyalan sun ce sun samu wannan bayanin ne ta hanyar tattaunawar waya da ‘yan ta’addan suka yi da su kwanan nan.

Waɗanda aka sace ɗin an yi garkuwa da su ne watanni da suka gabata, bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai ƙauyen Woro, inda suka kashe mutane da dama tare da yin awon gaba da mata da yara 176.

Wani dangin waɗanda aka sace ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun ce sun koyar da waɗanda suke riƙe da su ilimin addinin Musulunci, ladabi da kuma haddar Alƙur’ani.

Wannan majiya ta ce ‘yan ta’addan sun yi alfahari cewa da yawa daga cikin mata da yaran sun kai matakin da za a iya cewa sun “kammala karatu.”

An ruwaito cewa, “Sun gaya mana cewa yawancin matanmu da yaranmu sun haddace sassa na Alƙur’ani kuma sun koyi darussa na addini.

Sun ce suna shirin yin bikin kammala karatu domin murnar abin da suka koya.”

Wannan majiya ta ƙara da cewa ‘yan ta’addan sun yi barazanar cewa duk kuɗaɗen da za su kashe wajen bikin za su ƙara su cikin kudin fansa da za a nemi gwamnati da iyalai su biya.

Wani dangi ya ce lamarin ya girgiza su matuƙa, yana mai cewa ba su san ko su yi kuka ko su ji tsoro ba.

Ya ce, “Waɗannan mutane ya kamata a ce an mayar da su ga iyalansu, amma yanzu ana maganar ‘graduation’ kamar suna nasu ne. Kowace rana da suka ƙara kasancewa a wurin, muna ƙara tsoron cewa ana ƙara rinjayar su da tunaninsu.”

Wani jagoran al’umma da ke da masaniya kan ƙoƙarin ganin an sako mutanen ya ce wannan sabon labari ya nuna tsawon lokacin da waɗanda aka sace suka shafe a hannun ‘yan ta’addan.

Ya ce hakan yana nuna tsananin wannan bala’i da kuma buƙatar gaggawar matakin gwamnati domin ceto su.

By ukarofi